Yawan ‘Yan Najeriya Cikas Ne Ga Ci Gaban Kasar – Sarkin Kano

0
372

Daga Usman Nasidi.

SARKIN Kano, Muhammadu Sanusi Lamido na II a jiya Litinin 7 ga watan Oktoba ya ce adadin mutanen da ke Najeriya nakasu ne ga ci gaban kasar.

Sarkin ya yi wannan furucin ne a wurin taro karo na 25 a kan tattalin arzikin Najeriya wanda ake gudanarwa a babban birnin tarayya Abuja.

Taron na tattalin arziki ya samu halartar babban malamin addinin kirista, Bishop Mathew Kukah da kuma Gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi.

Hakazalika taron ya tattauna ne a kan yadda za a dada fito da sabbin hanyoyin bunkasa kasuwanci ta yadda zai kasance mutane za su iya gudanar da shi cikin tsanaki.

Sarkin ya ce, yawan mutanen da ke Najeriya nakasu ne ga ci gaban kasar saboda har yanzu babu wani abu na amfani da yawan mutanen ke kawo wa kasar.

Sanusi ya kara da cewa, akasin abubuwan ci gaba yawan ke kawowa kamar su, garkuwa da mutane, fashi da makami, rikicin makiyaya da manoma da kuma ta’addancin ‘yan bindiga.

Sarki Lamido ya ce: “Mutane da dama na maganar cewa yawan tamkar jari ne mai tsoka ga kasarmu, amma sai dai kash har yanzu ba mu kai wannan matakin ba. A halin yanzu zai iya cewa yawan mutanen kasar nan matsalace babba a gare mu saboda ban da yawaitar ayyuka marasa kyau babu abin da yawan ke haifarwa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here