Ba Shugaba Buhari Ne Yake Bayar Da Arziki Ba-Sheikh Jingir  

0
372

Isah  Ahmed Daga Jos

SHUGABAN Majalisar Malamai na kungiyar Jama’atu Izalatin Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah ta kasa, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya bayyana cewa Allah ne yake bayar da arziki, ba shugaban kasa Muhammad Buhari ba, kamar yadda wadansu suka dauka. Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir, ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da nasiha a masallacin juma’a na  ‘yan taya, da ke garin Jos a ranar juma’ar da ta gabata.

Ya ce duk wanda ya ce shugaban kasa Buhari ne yake bayar da arziki, imaninsa bai cika ba. Domin babu mai bayar da arziki sai Allah, da ya hallicemu.

Ya ce  wallahi da yadda shugaban kasa  Buhari yake so ne a Najeriya, da yanzu babu sauran matsalar tsaro a Najeriya kuma da yanzu ayyukan hanyoyin mota da sauran abubuwan kyautata rayuwar al’umma sun cika kasar nan.

‘’Don haka mu yi hankali da miyagun ‘yan siyasa masu bata tunanin mutane. Wallahi gara yanzu da lokacin da ake jefa mana bama-bamai a kasar nan. Don haka gwamnatin  shugaban kasa Buhari, ta fi gwamnatin da ta gabata’’.

Sheikh Jingir ya nuna goyan bayansa kan rufe kan iyakokin kasar nan, don hana shigo da miyagun kwayoyi da makamai da shinkafa.

Ya yi kira ga al’ummar kasar nan kada su yarda a rika zagin shugaba kasa da ma’aikatan hana fasa kwauri, kan wannan aiki da ake yi na hana shigo da miyagun abubuwa zuwa kasar nan. Ya ce babu shakka  miyagun kwayoyin da ake shigo da su kasar nan, suna cutar al’ummar kasar nan, don haka yakamata jama’a su yi tunani kan wannan al’amari

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here