Kotun Majistare Ta Tsare Malamai A Gidan Kaso A Jihar Kaduna

0
383

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

WATA karamar kotun Majistare da ke aiki a Kaduna ta tsare Malamai shida na makarantar musuluncin nan na Ahmad Bn Hambal Islamiyya da ke cikin garin Rigasa da ‘yan sanda suka kama.

An gurfanar da Malaman addinin a kotun Majalistare na 16 da ke Kaduna a gaban Alkali Musa Lawal Mohammed.

An shigo da wadannan Malamai harabar kotu ne da karfe 1:00 inda aka soma zama da karfe 2:00 na rana. Alkali mai shari’a Musa Lawal Mohammed ya kuma tashi ne da bayan sa’a guda da rabi.

Wadanda aka gurfanar a gaban kuliya sun hada da; Ismail Abubakar, Umar Abubakar, Abdul’azeez Adam, Abubakar Muktar. Ragowar su ne; Abdullahi Auwal da kuma Salisu Ibrahim.

Lauyan hukumar ‘yan sanda, Hassan M Malan, ya fada wa kotu cewa ana zargin wadannan mutanen ne da kitsa laifi, tsare mutane, da kutun-kutun da kuma mugunta da yin ba daidai ba.

Hassan .M. Malan ya kuma sanar da Alkalin kotun cewa yanzu haka ‘yan sanda suna ci gaba da binciken laifukan wadanda ake zargin. A nasa bangaren, Lauyan wanda ake tuhuma, ya kare su.

Sani Shehu Surajo wanda shi ne ya tsaya wa wadanda ake zargin ya fada wa kotu cewa babu wata kwakkwarar hujja da ke nuna wadanda ake tuhumar sun aikata laifukan da ake jefe su da su.

Lauyan da ke kare wadanda ake zargin, Shehu Surajo ya yi kokarin rokon kotu ta ba da dama a saki wadannan bayin Allah daga cikin gidan yari, a ci gaba da bincikensu a ofishin ‘yan sanda.

Mai kare hukuma ya mayar da martani cewa ragar hukumar ta cika don haka a ci gaba da tsare su a kurkuku. Dayan Lauyan ya ce zai nemo beli a babbar kotu bayan dage karar zuwa 29 ga wata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here