EFCC Ta Gano Naira Miliyan 65.5 A Ofishin INEC Na Zamfara

0
345
Rabo Haladu Daga Kaduna
HUKUMAR EFCC ta ce ta bangado fiye da naira miliyan 65.5 a ofishin zaben jihar Zamfara da ke birnin Gusau.
Hukumar ta sanar cewa ta samu kudaden ne a cikin wasu akwatunan adana kudi masu sulke a ofishin akanta da mai kula da kudin hukumar ta INEC.
Kudin dai sun hada da bandir-bandir guda 81 na naira dubu-dubu da bandir 97 na ‘yan dari biyar-biyar da kuma 500 guda 96.
A ta bakin hukumar EFCC da ke jihar Sokoto wadda ita ce ta kai samamen ta ce ta samu korafi ne daga wani ma’aikacin wucin gadi da ya yi aikin zaben 2019 a jihar amma ba a biya shi hakkinsa ba.
Ma’aikacin ya yi zargin cewa ba su samu alawus ba na naira 6000 na aikin zabe da suka yi guda biyu ba
EFCC ta ce tana zargin kudin na daga cikin kudaden da gwamnati ta saki ga hukumar zabe domin yin aron kujeru da rumfuna ga rumfunan zabe sannan kuma a biya ma’aikata.
Har kawo yanzu dai hukumar INEC ba ta ce uffan ba dangane da batun.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here