A’isha Buhari Ta komo Gida Najeriya

0
734

Daga Zubairu Sada

A tattaunawar da ta yi da manema labarai jim kadan bayan saukarta a filin jirgin sama na Abuja, A’isha Buhari ta yi watsi da jita-jitar da aka rika bazawa cewa ta yi yaji ne inda ta ce ta tafi ne domin a duba lafiyarta sannan kuma ta samu lokaci da ‘ya’yanta.

A ranar Juma’a da daddare ne Aishar ta wallafa wani hotonta tare da mai dakin jakadan Najeriya a Birtaniya Mrs Modupe Oguntade, a shafinta na Instagram suna yin ban-kwana gabanin tashinta zuwa gida.

A hoton da ta wallafa, ta yi godiya ga mai dakin jakadan, wadda ta ce ta rako ta ne, domin kamo hanyar komawa gida.

Tun a watan Agusta ne dai mai dakin shugaban kasar ta bar Najeriya zuwa aikin hajji a kasar Saudiyya, wadda daga bisani rahotanni suka ce ta wuce zuwa birnin Landan na Birtaniya.

Tsawon lokacin da ta kwashe ba tare da an gan ta a bainar jama’a ko kuma wasu wuraren taruka kamar yadda ta saba ba, ya janyo muhawara a tsakanin al’ummar kasar, inda wasu rahotanni ke cewa hakan ya faru ne saboda wani sabani da ya faru tsakaninta da wasu na kusa da shugaban, sai dai BBC ba ta iya tabbatar da sahihanci wannan magana ba.

Haka nan kuma babu wata kafa a hukumance daga gwamnatin kasar da ta yi wani karin bayani game da lamarin.

A baya bayan nan dai A’isha Buharin ta tofa albarkacin bakinta kan wasu muhimman abubuwa da suka faru a kasar ta Najeriya, wadanda suka hada da Allah-wadan da ta yi da dabi’ar wasu malaman jami’a da aka bayyana a wani rahoto na BBC suna neman yin lalata da dalibansu.

Haka kuma ta yi wani tsokaci a lokacin bikin ranar tunawa da ‘ya mace ta duniya, wanda duk kafin wadannan an jima ba a ji duriyarta ba, kamar yadda aka saba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here