An Gano Man Fetur A Yankin Arewa Maso Gabas – NNPC

0
320

Daga Usman Nasidi.

HUKUMAR kamfanin man fetur ta Najeriya (NNPC) ta sanar da cewa an gano mai a yankin arewa maso gabashin kasar.

Mukadashin manajan sashin hulda da al’umma na kamfanin, Samson Makoji ne ya bayar da wannan sanarwar a ranar Juma’a.

Ya ce gano man fetur da iskar gas masu yawa da aka yi a yankin Gongola “zai janyo masa saka hannun jari zuwa kasar kuma zai samar wa al’umma ayyukan yi da inganta kudaden shiga da gwamnati ke samu.”

Sanarwar ta ce, hukumar NNPC tana sanar da gano bakin mai masu yawa a Rafin Kolmani II da Upper Benue ta dalilin, Gongola Basin a yankin arewa maso gabashin kasar.

Idan ba a manta ba shugaba Muhammadu Buhari ne ya kaddamar da fara hakar mai a rafin Kolmani II a ranar 2 ga watan Fabrairun 2019.

Makoji ya yi bayanin cewa an haka daya daga cikin rijiyoyin har sai da ya kai zurfin kasa 13,701 wadda hakan ya sa aka gano man fetur da iskar gas a matakai daban-daban.

Ya ce a ranar Alhamis, daya daga cikin ma’ajiyarsu ta fashe kuma, ‘ bakin mai ya fara ambaliya misalin karfe 9.20 na dare wadda hakan ya sa aka kone gas din da ke ciki domin kare aukuwar matsala a wurin hakar man.”

Makoji ya ce NNPC za ta yi amfani da sabbin dabaru na zamani domin kiyaye haddura da za a iya haduwa da su inda ya kara da cewa kamfanin na shirin fara hakkar wasu rijiyoyin a Gongola Basin.

Ya kuma ce za a mayar da hankali da yankunan da ake kira Dahomey da Anmbra Basin da tuni an samu man fetur da iskar gas a wurin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here