Jita-jitar Yin Yaji Bai Ba Ni Mamaki Ba – Ai’sha Buhari 

0
523
Mustapha Imrana Abdullahi
UWARGIDAN shugaban kasar tarayyar Nijeriya Hajiya Ai’sha Buhari ta bayyana cewa duk irin jita-jitar da ake yadawa a kafafen sada zumunta na batun yin yaji da kuma mijinta zai yi aure duk ba su zo mata da mamaki ba.
“Saboda a lokacin da mijina ba shi da lafiya ya tafi neman magani akwai wadansu mutane da ke yada hoton gawa a yanar gizo, sun yi ta yadawa cewa ga hoton gawarsa, lokacin wadansu matan shugabannin wadansu kasashe sun yi ta kirana suna tambaya shin me yake faruwa ne, sakamakon hakan na kira shugabannin bangaren sadarwa na kasa kamar NCC da NBC da kuma NOA wato hukumar wayar da kan jama’a ta kasa da dai makamantan su, na shaida masu cewa to wadanda suke yada irin wannan abu za su kai mu inda ba za mu iya fitowa ba”.
Ta ci gaba da cewa masu yada wannan hotuna a yanar gizo duk an san su amma an bar su suna yada abin da suke so.
Matar Buhari ta ci gaba da cewa masu yada batun Buhari zai yi aure ai ba ita ce aka ce za ta yi aure ba domin ita da man tana da aurenta, amma abin da ta sani shi ne ta je hutu kamar yadda suka saba zuwa kusan kowace shekara kuma daga can ta ji jikinta ya yi mata dan nauyi ta ga Likita, ya kuma ba ta shawara da ta dan samu hutu a kan ayyukan da take yi, don haka ban san abin da ake yadawa ba.
Ta yi godiya ga maigidanta bisa goyon baya da kuma yadda ya nada masu taimaka mata a wadansu bangarori.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here