Sarakuna Biyar Da Hakimai 33 Na Cikin Matsala A Zamfara 

0
511

Mustapha Imrana Abdullahi

KAMAR yadda kwamitin Jihar Zamfara a karkashin Gwamna Alhaji Muhammad Bello Matawallen maradun,ta kafa kwamiti domin gano irin yadda matsalar tsaro ta yi kamari. Kwamitin binciken ya bayar da shawarar cewa lallai ya dace a sauke wadansu Sarakuna guda biyar tare da Hakimai 33 saboda irin rawar da suka taka a batun matsalar tsaron ‘yan bindiga a fadin Jihar.

Da yake gabatar da rahotonsa ga Gwamna Bello Matawalle, a cikin gidan Gwamnati, shugaban kwamitin tsohon shugaban ‘yan sandan Nijeriya Mohammed Abubakar ya ce kwamitin ya bayar da abubuwan da suka kamata a yi guda 132 da gwamnatin jiha da tarayyar ya dace su yi.

Mohammed Abubakar ya ci gaba da cewa a kokarin su na ganin an gano gaskiyar lamari, sun yi taron sauraren jama’a daga baki dayan kananan hukumomi 14 a jihar.

Ya kuma ce sun samu yin magana da mutane dubu hudu da suka hada da ‘yan bindigar da suka tuba, inda ya tabbatar da cewa daga shekarar Yuni 2011 zuwa Mayu 2019 an samu salwantar rayuka dubu 6,319 kuma mata dubu 4,483 ne suka zama Zawarawa sai kuma yara dubu 25,053 suka zama marayu a jihar.

An kuma samu salwantar da asarar makudan kudin da aka ba ‘yan bindiga matsayin shiyyar wadanda aka sace da suka kai Biliyan uku domin fansa a saki wadanda aka kama.

Kwamitin kuma ya fitar da cewa lallai ya dace Sarakuna biyar tare da Hakimai 33  a cire su domin samunsu da hannu a cikin matsalar ‘yan bindiga.

Kwamitin ya kuma ce akwai Sarki tare da Hakimai guda biyu ya dace a ba su lambar yabo ta kasa saboda irin kokarin da suka yi wajen tabbatar da tsaro a yankunansu.

Da yake tofa albarkacin bakinsa Gwamna Muhammad Bello Matawalle gode wa kwamitin ya yi bisa kokarin da suka yi na aikin binciken ganin jihar Zamfara ta zama lafiya.

Ya kuma ba su tabbacin cewa Gwamnati za ta tabbatar da yin aiki da dukkan abubuwan da kwamitin ya bayyana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here