Sarki Sanusi Ya Yaba Wa Ganduje A Kan Shirin Bayar Da Ilimi Kyauta A Kano  

0
442

Daga Usman Nasidi.

SARKIN Kano, Muhammadu Sanusi II ya yaba wa Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano saboda bullo da shirin ilimin frimare zuwa sakandare na kyauta a jihar duk da sa-in-sa da ke tsakaninsu.

Sanarwar ta mai magana da yawun Gwamnan, Abba Anwar ya fitar a ranar Juma’a ya ce Sarkin ya yaba wa Gwamnan kan shirin inda ya ce, “Na yi imanin cewa an kaddamar da wannan shirin ne domin yi wa Kanawa da al’umma hidima.”

Sanarwar ta ce an jiyo Sanusi na cewa, “Wannan shi ne irin abin da kasar nan ke bukata. Ya kamata mu mayar da hankali kan cimma wannan shirin domin ilimi shi ne turbar ci gaban kowace al’umma.

“Abin da Gwamnan ke yi abin koyi ne kuma an yi ne domin ci gaban al’ummarmu, kuma ina fatar wasu jihohin za su yi koyi da irin salon mulki na mai girma Gwamna.”

Sanarwar ta kuma ce ya kamata gwamnoni da sauran masu ruwa da tsaki su hada kai wuri guda su tabbatar cewa al’ummarsu sun zama abin alfahari ba nauyi a gare su ba.

Ya ce, “Kamar yadda Gwamnan ya nuna ya kamata yawan al’ummar mu ya zama alheri a gare mu ba nauyi ba.”

Sarkin ya shawarci dukkan jihohin Najeriya su rungumi shirin da ya ce ‘babbar hanya ce ta yi wa al’umma hidima.”

Mista Anwar ya ce sarkin ya yi wannan yabon ne lokacin da Gwamnan yake ganawa da wata tawaga daga Zenith Bank karkashin jagorancin shugaban yankin Arewa maso Yamma, Sani Yahaya a gidan gwamnati kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here