SHIRIN BAYAR DA ILIMI KYAUTA KUMA DOLE A JIHAR KANO ABIN KOYI NE

0
603
A daidai tsakiyar kamfen na kyamar ilimin zamani na boko da wata kungiyar ‘yan ta’adda suke yi a wasu jihohin arewa, sai ga shi jihar Kano, a arewa maso yammacin wannan kasa sun fito da wani tsari na tilasta zuwa makarantar firamare kuma kyauta daga matakin firamare zuwa sakandare.
Hakan ba karamar hobbasa ba ce wacce ta ke neman samun kwaikwayo daga daukacin jihohin arewa. Ya kamata jihohin nan su yi koyi da jihar Kano kan wannan babban al’amari da jihar ta sa a gaba.
Wannan babban al’amari da a ka kaddamar a jihar ta Kano kwanakin baya ya samu halartar Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo da kwararru a harkar ilimi da manyan masana a harkar ilimi da kungiyoyin kasa-da-kasa na duniya. Cikin wadanda suka samu halartar wancan bikin kaddamarwa har da Jakadun kasashe kamar su Sa’udiyya, Masar, Amurka, Hadaddiyar Daular Larabawa, da dai sauransu.
Daga cikin wakilan manyan kungiyoyin nan na kasa-da-kasa da akwai daga DFID, UNESCO, USAID da sauran irinsu. Wadanda kowannensu ya nuna cewar a shirye suke su bayar da goyon bayansu dari bisa dari wajen ganin wannan gagarumin shirin ya samu nasara.
Lokacin bikin, a jawabinsa Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje cewa ya yi “Babban dalilin yin shi wannan taro na ilmantarwa kan wannan manufa ta gwamnatinsa an yi shi ne saboda ana son a tattauna yadda za a samar da hanyoyin aiwatar da wannan manufa ba tare da samun wani tsaiko ba.”
Ya kuma kara tabbatar da cewa shi wannan shiri yana daga cikin alkawurran da ya yi wa jama’ar jihar ta Kano lokacin da ake rantsar da shi a dawowarsa kan karagar mulki jiko na biyu. A lokacin ne ya ambata cewar “Wannan gwamnatin ta dauki aniyar aiwatar da shirin bayar da ilimi kyauta kuma dole a matakan firamare da kuma na sakandare.”
Kuma yadda aka samu halartar manyan Jakadu da kusohin wasu manyan kungiyoyin bayar da tallafi na kasa-da-kasa yana nuni da cewar wannan gagarumin aikin da Gwamna Ganduje ya dauko ba shi kadai ba ne zai fuskanci wannan abu da niyyar magance dukkan matsalolin da ke tattare da shirin ba.
Kuma lallai jihar Kano karkashin Ganduje ba karamin hobbasa ta yi ba. Wannan kuma shi ne yake nuna daura damara ta gaske da wannan gwamnatin ta yi, tare da tabbacin cewa an shirya tsaf domin samun nasarar shirin. Duka dai saboda a yi maganin babbar matsalar nan ta mayar da yara makarantu, wadanda suke shekarun shiga makaranta.
Akwai ciwo da takaici idan muka kalli alkaluman nan da suke sanannu cewar Najeriya tana da sama da Milyan da dubu dari biyar wadanda ba sa zuwa makaranta. Mafi munin kuma shi ne idan aka yi la’akari da cewar kashi 60 daga cikinsu yara ne mata.
Sa’annan yara Milyan takwas ne daga cikin wancan kason da suke daga Arewacin wannan kasa, tare da cewar kaso mafi yawa daga cikinsu daga jihar Kano suke. Ana maganar sama da Milyan uku.
Amma fa bincike daga baya ya nuna cewar akwai da yawa daga cikin wadannan Almajirai da suke daga makwabtan kasashen Nijar da Kamaru da Chadi. Saboda domin a samu maganin wannan matsala kacokan ya kamata a ce an samu wani shiri na doka wanda jihohin Arewa za su yi hadin gwiwa wajen magance wannan matsala.
Kamar dai yadda a kullum Gwamna Ganduje yake kira da samar da wata hadaddiyar hanya mikakkiya daga jihohin Arewa a hade su. Wanda a dalilin samar da wata mafita mai dorewa kan harkar Almajirci da magance rashin zuwa makaranta ga yara, gwamnatin jihar Kano ta kafa wani kwamiti na musamman na ganin an aiwatar da gudanar da wannan manufa mikakkiya.
Yin hakan kuma zai inganta wani shiri ne na musamman da tsarin nan mai kula da shirin inganta rayuwar yara na Majalisar Dinkin Duniya, wato UNICEF karkashin wani shiri na musamman na ganin an kara inganta samar da ilimi na yaran da aka mayar zuwa makarantu, wato BESDA.
Tattare da wannan kuma akwai daya shirin na inganta harkar karatun Tsangayu da Islamiyoyi. Wanda a halin da ake ciki da akwai ire-iren wadannan makarantun sun kai 13,619, wanda suna da yara dalibai sama da Milyan biyu da rabi.
Kuma saboda a tafiyar da wannan shiri cikin cin nasara da kulawa ta musamman, hakan ta sa gwamnatin jihar ta Kano ta samar da wata hukumar kula da makarantun Kur’ani da makarantun Islamiyyah. Hakan ya sa aka samar da wata hanya mikakkiya kuma ingantacciya wajen kula da ingancin tafiyar da harkokin makarantun da kuma maganin duk wani kalubale da zai iya tasowa.
Kamar yadda rahotannin suka same mu, an bayyana cewar gwamnatin jihar Kano ta soke biyan duk wasu kudaden makarantun sakandare da da can iyayen dalibai suke biya tun daga watan Satumbar 2019. Haka nan kuma gwamnatin ce yanzu za ta dinga biyan kudaden kula da wadannan makarantu.
Yawan makarantun ya kai 1,180 da dalibai guda 834,366. Kuma yadda lissafin yake gwamnati za ta kashe Naira Milyan 200, a duk wata. Wanda hakan shi yake nuna cewar a shekara za a kashe Naira Milyan Dubu Biyu da Milyan Dari Hudu (N2.4b).
Shi fa wannan shirin na bayar da ilimi kyauta kuma dole yana da matukar amfani ga wannan kasa tamu ta Najeriya, musamman saboda wasu bayyanannun dalilai. Misali shekaru uku kenan yau cif bayan gabatar da shirin nan na tabbatuwar muradun karni na 4, har zuwa yanzu babu wata gagarumar nasara da za ka ce an samu wajen rage yawan yaran da suke gararamba kan tituna ba tare da zuwa makaranta ba. Tare da matasa da kuma wadanda suka dan data.
Kamar dai yadda Cibiyar Kididdiga ta UNESCO ta ambata cewar a sashen Afirka ta yamma akwai yara da matasa wadanda yawansu ya kai Milyan 258 da kuma dubu 400 ba sa zuwa makaranta a wajejen karshen shekarar 2018. Rahoton kuma ya kara bayyana cewa a shekarun bayan dai wannan bangaren namu na Afirka shi ne yake dauke da kaso mafi yawa na yaran da da sa zuwa makaranta.
Daga cikin yara su Milyan 59 wadanda suke da shekarun zuwa makarantun firamare amma ba sa zuwa, da yawa daga cikinsu sun fito ne daga wannan sashen namu na Afirka. Wasu su kimanin Milyan 32 ko kuma ma a ce sama da rabin wadanda su ke a wannan bangaren namu.
Sannan kasashen kudancin Asiya suke mara mana baya wajen yawan yaran da ba sa zuwa makaranta. Sun kai Milyan 13. Sa’annan kuma dai wannan bangaren namu na Afirka mu muke da mafi yawan yaran da ake danne masu hakkinsu na zuwa makaranta.  Wanda kaso 19 cikin 100 ake tauye masu wannan hakkin nasu.
Daga nan kuma sai Arewacin Afirka wadanda suke da kaso 9 cikin 100 na irin wadannan yara. Sai kuma Kudancin Asiya masu kaso 7 cikin 100. Saboda haka akwai bukata ta gaggawa saboda magance wannan matsala. Sa’annan kuma duk da cewar ilimin firamare kyauta ne kuma dole a wannan kasa ta mu, amma duk da haka kusan yara Milyan 10 da dubu 500 ba sa zuwa makaranta, kamar yadda hukumar UNICEF ta fada.
Abin lura a nan kuma shi ne, yawaitar wadannan yara ba zai haifar da da mai ido ba ga ci gaban kasa. Saboda haka ba ma amfanin ai ta ranto kudade a na ta faman yin wasu gine-gine. Bayan ba a mayar da hankali wajen gina zukatan jama’ar da za su yi amfani da wadannan abubuwan raya kasar ba. Saboda haka yaran da ba a gina zukatansu ba, su ne kuma wadanda idan sun taso za su yi fancakali da wadannan abubuwan.
Hanya mafi sauki da kyau ga jihohin Arewa wadanda su ka fi wannan matsala shi ne, a samar da wani yanayi da za a kara shigar da tsarin manhajar karatun Islamiyyu da Tsangayu da yadda tsarin manhajar matakin gwamnatin tarayya yake. Ta haka ne za a gyara tare da tseratar da yanayin karatun Islamiyyu da na Tsangayu yake. Kamar dai yadda jihar Kano take yi a halin yanzu din nan.
Wani kuma abin ban sha’awa shi ne yadda Kano karkashin Ganduje ta taso haikan domin cimma wannan manufa, ya kasance wata hanya ce ko ‘yar manuniya cewar Kano ta amsa kiran da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi na cewar jihohin Arewa su tashi tsaye wajen kara gyara harkar ilimin makarantun Islamiyya.
Hakan kuma ya yi daidai da shirin nan na dokar hakkunan yara mai suna “2003 Child Rights Act” wanda a ka ambaci cewar samar da ilimi ga yaro yana daga cikin hakkinsa na dan Adam. Saboda haka ya zama wajibi a yaba wa gwamnatin jihar Kano saboda wannan babbar hobbasa da suka yi, na mayar da yara makaranta. Wannan ba karamar dabara ba ce ta gina rayuwar wadannan yaran ta nan gaba.
Ya kuma zama wajibi ga gwamnatin jihar Kano ta fahimci cewar wannan gagarumin shiri na janye yara daga kan titi a hana su gararamba, sannan a sa su ko a mayar da su makarantu abu ne wanda ya fi karfin fada da baki kawai. Musamman ganin yadda matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta ya addabi wannan sashe namu na Afirka. Kamar kuma yadda masana da kwararru ma suka fada.
Daga cikin matsalolin da ake danganta wannan tabarbarewar ilimin yara da su sun hadar da rashin isassu da kuma kwararrun malamai a wadannan makarantu da kuma rashin kayan koyarwa din gami da kyakkyawan yanayin koyarwar.
Haka nan an kara da cewar akwai dalilan kasancewar zaman yaran a irin kauyukan nan na can ciki wadanda harkokin more rayuwa su ke karanci da kuma irin yaran nan da suke da wata tawaya a halittarsu gami da irin yaran da ke wajen sansanin ‘yan gudun hijira haka.
Sannan an gano cewar hatta shi kan sa wajen neman ilimin, muddin ba a neme shi ta yadda ya kamata ba, watakila saboda rashin sanin yadda ya kamata a neme shi kuma mai inganci. Hakan ma ya kan haifar da rashin zuwan yara makaranta.
Hatta ma yadda wasu ke ganin sam-sam ma bai kamata a neme shi ba, ana ta sukarsa, misali a nan shi ne na ‘yan kungiyar nan ta Boko-Haram, wacce ta ke ganin haramci ma na gaba daya kan neman ilimin. Wanda su ana su wajen ma wai shi wannan ilimi ba wani abu ba ne illa harkar shedanci, su a wajen su. Kamar yadda abin ya yi kamari a Arewa Maso Gabashin Najeriya.
Sannan ma akwai maganar ware wata karamar kabila wajen bayar da shi wannan ilimi. Duk wadannan dalilai ne da suke sa yara su guje wa makaranta. Sannan kamar a Kudu maso gabashin Najeriya, su kuma a irin na su tunanin, samun ilimi ba ya cikin abubuwan da suke tallafar rayuwar mutum ya zama mai dogaro da kansa. A wajen su. Bangarorin kasar dai kowanne akwai irin nasa tunanin kan samar da ilimin zamani.
Akwai tunani mai karfi game da cewar rashin kula da iyakokin kasar nan sosai wajen kula da bakin haure, ya na kara tallafar yanayin nan na haifar da tururuwar yaran da ba sa zuwa makaranta. Kamar dai yadda gwamnan Kano Ganduje ya bayyana cewar mafi yawa daga cikin irin wadannan yaran da ke gararamba ba zuwa makaranta, wasunsu ma daga kasashen ketare suke shigowa jihar ta Kano.
Saboda haka babban abin lura a nan shi ne, yin maganin wannan matsala abu ne da yake bukatar tallafin bangarori daban daban. A kan haka ya zama wajibi gwamnatin Ganduje ta samar da wani yanayi da zai kara inganta makarantu tare da samar da kayan aiki na zamani da kyawawan wuraren koyarwa, tare da horaswa kan horaswa na malaman da suke karantarwa a wadannan makarantu. Tare kuma da dukkan wasu hanyoyin da za su kara inganta koyo da koyarwa.
Sanoda haka mu na kira ga ragowar jihohi da su yi koyi da jihar Kano kan irin wannan hobbasa da jihar ta faro tun daga lokacin da Gwamna Ganduje ya kaddamar da wannan kyakkywan shiri na inganta harkar ilimin. Hakan yana cikin abubuwan da za su kara tallafa wa al’umma a nan gaba. Rashin hakan kuma yana nuni ga wata sangarta da lalacewar al’amurra a nan gaba.
Ya kamata a fahimci cewar akwai wata alaka mai karfin gaske tsakanin ingantaccen ilimi da kuma ci gaban tsarin mulkin Dimokuradiyya. Kamar yadda tsohon dan gwagwarmayar nan kuma tsohon shugaban kasar Afirka Ta Kudu, Nelson Mandela ya ce ne “Lafiya da kuma ci gaban mulkin Dimokuradiyya ta na samuwa ne ta hanyar samar da al’umma mai ilimi kuma wacce take kanta a waye.”
Wani abin lura kuma shine, shi fa ilimi wani doki ne da ya ke dauke da ma’anar ainihin karfafa al’umma su san menene ya ke musu ciwo, tare da ba su damar yin zabin da suke so a rayuwarsu ba tare da wani ya zare masu idanu ba.
Hasali ma shi ilimi shi ne yake ba al’umma dama su tambayi shugabanninsu ta yaya suke tafiyar da alhakin da a ka dora musu a matsayin shugabannin jama’a. Wanda hakan yana kara inganta samar da shugabanci da shugabani masu adalci.
Kuma alhakin gwamnatin jihar Kano ne su yi duk mai yiwuwa wajen kara fadakar da iyayen yara, musamman wadanda su ke a karkara da kuma iyayen da su ba su yi karatu ba, cewar ilimim firamare har zuwa sakandire kyauta ne fa. Watakila za ka samu duk abin nan da a ke ta magana a kai, su ba su ma san kyauta ba ne ilimin. Wannan ya na da muhimmanci kwarai da gaske.
Wani kuma babban abin lura a nan shi ne, saboda gudun kar yaran da ba na nan ba su yi ta tuntudowa jihar Kano saboda ganin wannan garabasa da gwamnatin Ganduje ta kawo, har ma ta kai wadanda aka yi saboda su su kasa cin gajiyar abin, ya zama dole jami’an shige da fice su kara mikewa tsaye wajen tantance gami da lura da wadanda ke shigo mana, a san daga ina suke, kuma ina za su je.
Sa’annan kwanaki ko watanni nawa za su yi a wuraren da suka zo. Saboda haka amfani da katin dan kasa da ragowar hanyoyin yin rajista ta ‘yan kasa take da muhimmancin gaske a wannan tafiyar da ma dukkan al’amurran da ke biyo baya.
Mai Fassara Abba Anwar, Babban Sakataren Yada Labaran Gwamnan Jihar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here