Wadanda Suka Yi Garkuwa Da Shugaban Makaranta A Kaduna Sun Nemi Naira Miliyan 20 Kudin Fansa

0
334

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

‘YAN bindigar da suka yi garkuwa da Shugaban makarantar sakandare na Government Technical College, Mararabar Kajuru, da ke karamar hukumar Kajuru, a jihar Kaduna, Mista Francis Maji, sun bukaci a biya kudin fansa naira miliyan 20.

Wata majiya ta kusa da makaranta ta bayyana a wayar tarho cewa masu garkuwan sun tuntubi iyalinsa ta dayan wayar shugaban makarantan inda suka gabatar da bukatarsu.

Wasu ‘yan bindiga a tsakar daren ranar Alhamis, ne suka kai mamaya makarantar sannan suka yi garkuwa da shugaban makarantar.

Rundunar yan sandan jihar Kaduna ta tabbatar da faruwar lamarin.

Garkuwar na zuwa ne mako guda bayan yan bindiga sun sace dalibai mata shida, da ma’aikata biyu a kwalejin Engravers College, Kakau Daji a karamar hukumar Vhikun da ke jihar.

Wani malamin makarantar da ya nemi a sakaya sunansa ya ce ‘yan bindigar da yawansu ya kai sama da 20 sun farma makarantar da misalign karfe 12:00 na dare sannan suka fara harbi a sama inda suka tafi da shugaban makarantar daga gidansa.

Majiyar ta ce daga iyalansa har hukumar makarantar ba su da hanyar biyan kudin fansar domin ceto shugaban nasu.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here