Asakala A Villa: Wace Ce Ta Dauki Bidiyon A’isha Buhari Tana Fada?

  0
  570

  BARAKA ta kunno kai a Fadar Shugaban Najeriya a daidai lokacin da ake yada jita-jitar cewa Shugaba Muhammadu Buhari zai yi wa matarsa kishiya.

  A ‘yan kwanakin nan wani bidiyo ya rika yawo a shafukan sada zumunta wanda a cikinsa aka ga uwargidan shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tana ta fada da harshen Turanci tana gaurayawa da Hausa.

  Jama’a da dama a shafukan sada zumunta sun rinka alakanta wannan bidiyon da cewa A’isha Buhari ce ta dawo daga Ingila tana fada cewa an rufe mata kofa.

  BBC ta samu jin ta bakin Aisha Buhari inda ta tabbatar da cewa ita ce aka dauka a cikin bidiyon amma ta ce tsohon bidiyo ne.

  Ta kuma yi karin haske cewa Fatima ‘yar gidan Mamman Daura ce ta nadi bidiyon da ake tafka mahawara a kai.

  Sai dai ko da BBC ta tuntubi Fatima Mamman Daura, ba ta musanta daukar bidiyon ba, sai dai ta ce ta dauki bidiyon ne domin ta nuna wa iyayenta da jami’an tsaro a matsayin shaida ko da wani abu ka biyo baya.

  Mene ne A’isha Buhari ta ce?

  Bayan saukar A’isha Buhari a filin jirgi a Abuja, ta samu ganawa da ‘yan jarida inda ta yi bayanai da harshen Hausa da kuma Turanci.

  A cikin bayanin da ta yi a harshen Turanci, ta bayyana cewa lallai ita ce a wannan bidiyo kuma lamarin ya faru ne a cikin fadar shugaban kasa da ke Abuja.

  Ta ce: “Jami’an tsarona suna wurin amma sun kasa yin komai domin ‘yar gidan Mamman Daura – Fatima ce ta dauki bidiyon kuma har yau ni da su mun kasa yin komai kan lamarin.”

  Haka zalika a hirar da aka yi a harshen Hausa ta nanata cewa Fatima ce ta dauki bidiyon, har tana yi ma ta dariya kuma ita ce ta rufe ma ta kofar dakin ajiyar kayayyaki.

  Mene ne Fatima Mamman Daura ta ce?

  A hirarta da BBC, Fatima ta bayyana cewa tun bayan hawan Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, shugaban ya bai wa mahaifinta (Mamman Daura) wurin zama a cikin fadar shugaban kasa wanda ake kira ”Glass House.”

  Ta ce a lokacin da Yusuf Buhari ya samu hatsari a kwanakin baya, Shugaba Buhari ya bukaci Mamman Daura da ya koma wani gida da ake kira ”House No. 8”, wato gida mai lamba 8 domin a yi jinyar Yusuf a gidan da Mamman Daura da iyalansa suke zaune domin wurin ya fi kusa da inda Aisha Buhari ta ke.

  Fatima ta bayyana cewa ko da hakan ya faru iyayenta ba su Najeriya, sai dai mahaifinta ya ba ta umarnin ita da ‘yar uwarta, cewa su kwashe kayansu daga gidan a ranar wata Asabar.

  Ta bayyana cewa suna cikin kwashe kayansu ne sai ta ji hayaniya, domin ita tana can cikin kuryar daki ‘yar uwarta kuma tana dakin waje wanda ya fi kusa da kofar shiga gidan.

  Ta ce kofar da ke waje an saka mukulli an rufe domin yawanci idan suna ciki su kan rufe ta.

  Ta bayyana cewa ko da Aisha ta zo ta ga kofar a rufe, ”ta yi amfani da kujerar karfe wajen balle kofar.”

  A cewar Fatima, wannan dalili ne ya sa ta dauko waya domin yin bidiyo don ya zama shaida.


  Shin akwai yar tsama tsakanin iyalin Mamman Daura da A’isha Buhari ne?

  An dade ana jita-jita musamman a kafofin sada zumunta cewa Aisha Buhari ba ta ga maciji da Mamman-Daura wanda yake amini ne ga shugaban kasa kuma dan uwansa ne na jini.

  Ko a wurin taro ta sha yin shagube kan wasu mutane da ake zargin sun zagaye shugaban kasa sun hana shi aiki duk da cewa ba ta taba ambatar sunansa ba.

  Amma da alama a wannan karon tura ta kai bango tun da har ta kama suna kuma ta ce an kasa yin wani abu sakamakon ‘yar gidan Mamman Daura ce.

  Ko da BBC ta tambayi Fatima Mamman-Daura ko tun can dama ana samun rashin jituwa tsakanin Mamman-Daura da Aisha Buhari, ta bayyana cewa kafin Shugaba Buhari ya hau kan karagar mulki, suna zumunci lafiya kalau, amma tun bayan nan ne komai ya sauya aka fara samun matsaloli.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here