Ba A Kai Wa Ofishin Jakadancin Nijeriya Da Ke Jamhuriyar Benin Hari Ba

0
372
Mustapha Imrana Abdullahi
SAKAMAKON irin yadda aka rika wadansu bayanai a kafafen yanar gizo ya sa aka jawo hankalin ma’aikatar kula da hulda da kasashen waje bisa wani faifan bidiyon da ke zagaya duniya a kafafen sada zumunta da ke nunin kai hari ga ofishin jakadancin Nijeriya a Jamhuriyar Benin.
Ma’aikatar kula da hulda da kasashen wajen Nijeriya ta bayyana cewa bidiyon tsoho ne da aka kai wa ofishin jakadancin Nijeriya hari a Dakar, kasar Senegal kuma lamarin ya faru ne a ranar 4 ga watan Mayu, 2013.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar da mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Nijeriya Ferdinand Nwonye ya sanya wa hannu a ranar Lahadi, 13 ga watan Oktoba, 2019.
Kuma tuni har an kama jagorancin kai wannan garin wanda hukumomin kasar Senegal suka yi kuma sun kai shi gaban miliyan an yanke masa hukuncin zaman gidan yari na watanni shida.
A saboda haka ne ma’aikatar harkokin wajen Nijeriya ke fadakar da jama’a cewa su yi watsi da wannan faifan bidiyon da wasu ‘yan a casa kowa ya rasa ke yadawa domin yin batanci kawai da nufin bata dangantakar kasashen Nijeriya da Benin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here