An Rufe Makarantu Sama Da 2000 A Neja

0
366
Mustapha Imrana Abdullahi
A kokarin dabbaka harkokin ilimi gwamnatin jihar Neja ta rufe makarantu masu zaman kansu da suka kasa cika cikakkiyar ka’idar da aka shimfida masu.
Gwamnatin ta bakin Abubakar Aliyu sakatare ne a ma’aikatar ilimi ya bayyana cewa an dauki wannan mataki ne sakamakon rashin cikakken ka’idar da aka shimfida tun farko kafin mutum ya bude makarantar.
Ya dai bayyana hakan ne lokacin da kungiyar masu makarantu masu zaman kansu suka kaimasa ziyara.
Abubakar Aliyu, ya ci gaba da cewa ka’idojin da mutanen suka kasa cikawa sun hada da rashin samar da wadataccen wurin mazugunni,rashin ruwansha da makewayi da kuma kayan koyo da koyar da daliban da ke makarantun.
Hakika gwamnatin jihar Neja ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen daukar matakin da ya dace domin dai dai ta al’amura a kodayaushe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here