Gwamnan Bauchi Ya Yi Karin Haske Akan Furucinsa Na Cewa Daga Allah Sai Jonathan

0
456

Daga Usman Nasidi.

GWAMNAN jihar Bauci, Sanata Bala Abdulkadir Muhammad, ya yi karin haske a kan furucin da ya yi kwanan nan wanda ya kawo ce-ce-ku-ce a ciki da wajen jihar cewa “bayan Allah, sai tshon shugaban kasa Goodluck Jonathan.”

Gwamnan ya yi furucin ne a lokacin kaddamar da kungiyar kamfen din jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na zaben Gwamnan jihohin Bayelsa da Kogi a sakatariyar jam’iyyar na kasa da ke Abuja.

An alakanta shi da fadin cewa, a iya saninsa bayan Allah to Goodluck Jonathan ne, lamarin da ya kawo cece-kuce a shafukan sadarwa.

Da yake jawabi ga manema labarai akan lamarin, kwamishinan labarai na jihar, Ladan Salihu, wanda ya yi karin hasken akan matsayar ubangidan nasa, ya bayyana cewa a koda yaushe Gwamna Bala Muhammed kan sa Allah da Annabi Muhammed a gaba kafin ya yi kowane furuci.

Ya yi bayanin cewa jawabin da gwamnan ya yi ba wani sabon abu ba ne kawai jawabi ne na siyasa sannan ya bata rai kan yadda aka canja fassarar abun har ta kai ana alakanta lamarin ga addini.

Ya bayyana cewa an yiwa furucin mummunan fahimta ne sannan kuma cewa baya dauke da ainahin sakon, inda ya kara da cewa kawai Gwamnan na yabon tsohon shugaban kasar ne wanda ya bayyana a matsayin gwaninsa a harkar siyasa da ya ba shi damar yi wa kasarsa hidima a matsin ministan Abuja a lokacin gwamnatinsa.

Kwamishinan ya roki masu tayar da fitina da su janye daga amfani da jawabin wajen cimma burinsu na siyasa domin a koda yaushe gwamnan zai kasance mai mutunta addininsa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here