Gwamnatin Tarayya Za Ta Gina Gidaje 30,000 A Sassan Najeriya Daban-daban

0
369

Daga Usman Nasidi.

GWAMNATIN tarayya ta bayyana aniyarta na ginin gidaje 30,000 a sassa shida na Najeriya, a matsayin hanyar rage fatarar muhallin da ake fama da ita a kasar.

Mukaddashin Daraktan hukumar gidaje ta gwamnatin tarayya, Umar Gonto ne ya fadi wannan maganar a lokacin da yake ganawa da kwamitin gidaje da muhalli na majalisar wakilai ranar Laraba 16 ga watan Oktoba.

Daraktan ya ce, ban da ginin gidajen da gwamnatin ke yi a wasu jihohin kasar nan . Gwamnatin za ta sake gina wasu gidaje 30,000 wadanda za a raba a sassa guda shida dake kasar.

A cewar Gonto gwamnatin za ta yi hakan ne domin rage fatarar gidaje da ake fama da ita a kasar nan. Tun a shekarar 2005 aka cire hukumar gidaje ta gwamnatin tarayya daga kasafin kudin kasa, inji Gonto.

Wannan dalilin ne ya sanya hukumar ta FHA ke amfani da ‘yan kasuwa domin yin ginin gidaje. Hakazalika, akwai shirye-shirye na musamman na samar da gidaje a Arewa maso Gabas a matsayin gudunmuwa ga ‘yan gudun hijira.

Ana shi jawabin, shugaban kwamitin gidaje na majalisar wakilai, Mustapha Bala Dawaki (APC, Kano) ya jinjina wa hukumar a kan irin kokarin da take yi na ganin cewa ta sanya farin ciki ga fuskokin ‘yan Najeriya.

Ya kuma kara da cewa, gwamnatin tarayya za ta bayar da biliyan N10 a matsayin tallafi ga hukumar domin ci gaba da ginin gidaje a fadin Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here