Kungiyar Kwallon Kafa Ta Zuru Sun Kai Wa Kabiru Rafi Ziyara 

  0
  485
  Mustapha Imrana Abdullahi
  KUNGIYAR kwallon kafa ta garin Zuru sun bayyana cewa sun kai wa dan takarar kujerar karamar hukumar Zuru ziyara ne domin kara karfafa dankon zumuncin da ke tsakaninsu tun asali.
  ‘Ya’yan kungiyar kwallon kafar sun bayyana cewa kasancewarsu matasa masu sarrafa kwallon kafa domin motsa jinin jikinsu suka ga ya zama wajibi su ci gaba da nuna wa Kabiru Muhammad Abubakar Rafi, cewa ana tare kasancewarsa na kowa wato mutumin jama’a da ke rungumar kowa domin tafiya tare a dukkan hali.
  Hakika wannan ziyara ce ta karin karfin gwiwa ga dan takarar kasancewa ba a cin zabe wato samun nasara sai da matasa.
  Hakan na bayyana cewa dan takarar na tare da jama’a domin tafiya tare.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here