Za Mu Tashi Jami’ar Jahar Kaduna Daga Inda Take – Gwamnatin Kaduna

0
440

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

GWAMNATIN jahar Kaduna ta sanar da manufarta na sauya wa jami’ar jahar Kaduna wuri daga inda aka santa zuwa kan babbar hanyar Zariya zuwa Rigachikun domin fadada jami’ar tare da bai wa dalibai damar samun isassun guraben karatu.

Kwamishinan ilimin jahar Kaduna, Shehu Mohammed Makarfi ne ya bayyana haka yayin wani taron babban zaure a kan kasafin kudin shekarar 2020 da ya gudana a jahar.

Kwamishinan yana cewa sauya wa jami’ar wuri zai bai wa mutane da dama damar kai wa ga jami’ar cikin sauki, sa’annan ya ce nan ba da jimawa gwamnatin za ta fara aikin gini a sabon wurin.

“Nan ba da jimawa ba za mu tashi KASU zuwa filinta na dindindin a kan hanyar Zariya zuwa Rigachikun, an tanadar da filaye don wannan aiki, kuma nan gaba kadan za mu fara aikin gini a filin, sabon wurin zai fi dacewa da karatu da koyarwar dalibai.

“Wannan matakin zai bai wa dalibai karin guraben karatu a jami’ar, kamar yadda matakin kara yawan kwasa kwasai a kwalejin kimiyya da fasaha ta jahar da ke Zariya zai haifar, hakazalika mun kara yawan kwasa-kasai a kwalejin ilimi ta gidan Waya da kuma kwalejin horas da malaman jinya.” Inji shi.

A wani labari kuma, rundunar ‘an sandan Najeriya reshen jahar Kaduna ta tabbatar da mutuwar mutum guda biyo bayan wani mummunan hari da wasu miyagu yan bindiga suka kai a garin Birnin Gwari, cikin karamar hukumar Birnin Gwarin jahar Kaduna.

Kaakakin rundunar, DSP Yakubu Sabo ne ya tabbatar da haka a ranar Juma’a, 18 ga watan Oktoba, inda ya ce yan bindigan sun kai farmakin ne da misalin karfe 11: 30 na safiyar Laraba a wani gidan mai da ke kauyen Doka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here