Jihar Kano Ta Fara Horar Da Mutane 1,200 Zababbu Da Nadaddu 

0
528
Mustapha Imrana Abdullahi
GWAMNATIN jihar Kano karkashin jagorancin Dakta Abdullahi Umar Ganduje ta fara horar da mutane 1,200 Zababbu da nadaddun da suka fito daga kananan hukumomi 44, ana dai ba su horon ne kan yadda za su san makamar aiki a kowane mataki domin gudanar da mmulki kamar yadda ya dace.
Shi dai wannan taron horarwar ana yin sa ne a garin Kaduna, daga cikin masu halartar taron sun hada da zababbun shugabannin kananan hukumomi, mataimakansu, sakatarori, daraktocin mulki,masu kula da harkokin kudi, zababbun kansiloli,nadaddun kansiloli da masu bayar da shawara daga dukkan kananan hukumomi 44.
Da yake tofa albarkacin bakinsa a wurin taron da aka yi a otal din Asaa da ke cikin garin Kaduna, babban sakataren ma’aikatar kula da kananan hukumomin jihar Kano Abba Ladan Kailani, ya ce babban makasudin yin wannan taron horarwa shi ne domin kowane mutum ya san aikinsa da kuma matsayinsa domin amfanin jama’ar kasa baki daya.
Babban sakataren ya ci gaba da cewa gwamnati na sane da irin matsalolin da ake samu a tsakanin ma’aikatan musamman wajen gudanar da aikinsu, hakan ne ya sa aka shirya wannan taron horarwa domin a ilmantar da su kowa ya san aikin da da yadda ya dace ya yi shi.
“Baki dayan ma’aikatan da ke tafiyar da harkokin mulkin kananan hukumomin Kano suna nan domin samun horon samun makamar aiki za kuma su yi tambayoyin abubuwan da ba su fahinta ba a yi masu bayani cikakke kan inda kowane aikinsa ya fara da inda na wani kuma shi ma ya fara da kuma samun abubuwan da ya dace su aikata da wadanda bai dace ba”.
Kailani ya ci gaba da bayanin cewa sun kira tsofaffin shugabannin kananan hukumomi, kansiloli da dai tsofaffin ma’aikatan kananan hukumomi tare da malaman manyan makarantu domin kowa ya bayar da nasa ilimin a game da batun tafiyar da harkokin mulkin kananan hukumomi.
Ya kuma yi godiya ga Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje bisa irin yadda ya dauki nauyin wannan taron horaswa.
Da yake tofa albarkacin bakinsa Daraktan kula da harkokin horaswa, daukar ma’aikata da kula da wadanda suka ajiye aiki, Musa Isa Kira, cewa ya yi mahalarta taron sun fito ne daga daukacin kananan hukumomi 44 na jihar Kano musamman daga bangaren mazabun ‘yan majalisar dattawa
Shugaban kungiyar shugabannin kananan hukumomin jihar Kano shugaban karamar hukumar Nasarawa Dakta Lamin Sani, cewa ya yi suna halartar wannan taro ne domin su kara fadakar da junansu kan ayyukan da suke yi a ofisoshinsu domin samun yadda ya dace su gudanar da ayyuka a matakin kananan hukumomi ta yadda za a ciyar da kasa gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here