An Sace Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda A Kaduna

0
377

Mustapha Imrana Abdullahi

RUNDUNAR ‘yan sanda ta kasa reshen jihar Kaduna sun tabbatar da sace wani babban dan sanda mai mukamin mataimakin kwamishina a kan titin Jos Barde.

Kamar yadda rundunar ‘yan sanda ta kasa reshen jihar Kaduna suka tabbatar a cikin takardar da ke dauke da sa hannun mai magana da yawun rundunar DSP Yakubu Sabo cewa hakika wadansu mutanen da ba a san ko su wane ne ba sun wuce da babban dan sandan.

DSP Yakubu Sabo ya bayyana cewa a jiya ne rundunar ta samu rahoton ta hannun wadansu jami’an ta da suke aiki karkashin tsarin tsaro na Operation Safe Heaven) cewa an samu wata mota kirar kamfanin Nissan Murano inda aka samu katin shedar aiki mai dauke da sunan ACP I Miss Rambo,wanda su ne babban jami’in ‘yan sanda na Suleja.

Takardar ta ci gaba da cewa an samu motar ne an ajiye ta kawai a daidai gadar Knock kan iyakar Jihar Kaduna da Nasarawa ana kyautata zaton an sace mai ita ne a kan titin Barde zuwa Jos a Dajin Knock.

Kamar yadda aka bayyana a cikin takardar tuni an rigaya an fara magana da wadanda suka sace shi suna neman a ba su kudin fansa kuma ana nan kan kokarin ganin an kubutar da da shi tare da kama masu laifin.

Kamar yadda mai magana da yawun rundunar ya ce kwamishinan ‘yan sanda CP Ali Janga ya tabbatar wa da jama’a cewa suna yin dukkan mai yiwuwa domin kubutar da wanda aka sacen.

Kwamishinan ya kuma yi kira ga jama’a da su ci gaba da taimaka wa ‘yan sanda da ingantattun bayanai da za su taimaki rundunar a fita daga cikin halin matsalar tsaron da ake ciki.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here