Daga Ni Sai Gajeren Wando Na Tsira Hannun Masu Garkuwa Cikin Ikon Allah – Malam Inusa

0
454

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

A ranar Alhamis din da ta gabata ne wani bawan Allah Malam Inusa Mai Rake mazaunin Sabon Garin Rigasa Kaduna, ya hadu da wani iftila’in fadawa hannun masu garkuwa da mutane wanda daga bisani Allah Ya yi masa gyadar dogo ya tsere cikin ikon Allah da addu’a daga hannun masu garkuwar ba tare da biyan kudin fansa ba.

Dattijon dan kimanin shekaru hansin da dori kuma yake sana’ar noman Rake wanda daga shi sai Gajeren Wando a jikin shi ya samu damar tserewa da tsakar dare, ya ci karo da miyagun ne ayayin da yaje gonarsa dake mai Giginya yin kewayen kayan amfanin gonar, wanda anan ne suka ci karo da shi kana sukayi awon gaba da shi da rana tsaka da misalin karfe biyun rana.

Da yake zantawa da wakilinmu, malam Inusa ya bayyana cewa babu wani abinda ya cece shi baya ga yin addu’ar da ya yi  tayi domin ko lokacin da yan ta’addar ke jibgar shi sunji mamakin yadda yake ta addu’o’i da kalmar shahada domin shi ya tabbata babu ta yadda za a yi ya tsira daga hannun su idan ba wani ikon Allah ba ta hanyar  yin addu’o’i don ba ya da kudin da za a ba su na fansa.

Ya ce “akalla mu uku aka tarar a wajen to amma ni kadai ne mai waya a hannu kuma daya mutumin dattijo ne sosai wanda dukda haka sai da suka shanya shi a rana yana kallon sama kusan na awa daya saboda ba ya da waya, a yayin shi kuma daya yaron wani mai turin baro ne wanda shi ya tsere.”

Ya kara da cewa masu garkuwa da mutanen akalla su shida ne kuma duk Fulani ne wanda suke zaune a wani gida a can cikin tsakiyar wani kungurmin dajin Maguzawa, dukda yake ba zai iya gane ko ina ne ba amma yana jin karar babura jefi-jefi domin Rigarsa aka yaga don rufe masa ido a yayin da suka kama hanyar zuwa cikin dajin kuma dogon wandon duk ya lalace saboda rashin hanyar dajin da ake ta jan shi suna tafiya, wanda hakan yasa ya kasance daga shi sai Gajeren wando ya rage a jikinsa.

“Kafin mu je, sai da suka fara tambaya na akwai kudi, sai na ce idan da ina da kudi zan zo nan, sai suka amsa mun da cewa za mu kashe ka kuwa idan babu su don mun kashe mutane da yawa wada basu dashi, sannan suka kara tambaya na ko ina da yara sai na ce masu e ina da yara uku, shi ne suka sake tambayata ko manya ne ko yara, na fada cewa kanana ne –inji shi.”

“Wato a yayin da dare ya yi bayan duk sun kwanta amma ni ina zaune ina ta addu’o’i sai Allah Ya ba ni ikon yin magana inda nake ta cewa ina son na yi bahaya to amma ba bahayan nake ji ba illa ina fada ne kawai na yi don na ga ko za su amsa, to jin sun yi shiru ne ya sa na yi yunkurin tserewa wanda Allah Ya ba ni sa’ar guduwa inda na tsinci kaina karshe kwalta na garin Rigasa da asuba tun bayan misalin karfe uku na daren da na tsere nake gudu a cikin dajin – inji shi.”

A cewarsa bayan isar su gidan, mutum daya kawai ya tarar wanda shi ma da alamun garkuwa da shi aka yi, dukda yake bayan sun tafi da shi sai da suka fara yi mishi tambayoyi na ciniki don sanin ko nawa za su iya samu wanda har suka  yi ciniki da shi tun daga kan naira miliyan biyar kafin su amince a kan naira dubu dari.

A karshe Malam Inusa, ya bayyana cewa Allah cikin ikonSa ya dawo da shi gida lafiya kuma bai ba ‘yan ta’addar masu garkuwar mutanen iko ko sa’ar cutar da shi ko iyalinsa ba ta kowace fuska dukda yake sun gana mi shi ukuba na wannan wunin lakocin da ya kasance a tare da su, don haka yake yi wa Allah godiya a kan hakan..

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here