Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar Da Zaben Uba Sani A Kan Abokan Takararshi

  0
  412

  Usman Nasidi, Daga Kaduna.

  KOTUN daukaka kara, reshen Kaduna a ranar Litinin, 21 ga watan Oktoba, ta tabbatar da zabe Sanata mai wakiltan yankin Kaduna ta tsakiya, Sanata Uba Sani.

  Da yake zartar da hukunci a kan karar da Honourabul Lawal Adamu na PDP wanda ya yi takarar kujerar tare da Uba Sani na APC ya shigar, Jastis A.O. Okojie ya yi watsi da karar a kan hujjar rashin inganci sannan ya kaddamar da dan takarar APC a matsayin wanda ya lase zaben kujerar Sanatan.

  Da yake jawabi ga manema labarrai a kan hukuncin kotun, daya daga cikin lauyoyin Uba Sani, Barista  Frank Ikpe (SAN) ya bayyana hukunci a matsayin mai cike da adalci sannan kuma cewa ya yi daidai da tsarin doka.

  A cewarsa hukuncin kotun daukaka karar ya tabbatar da hukuncin kotun zaben sannan ya yi bayanin cewa alkalan sun tabbatar da hukuncin akan lamura uku wanda suka hada da ko Uba Sani ya cancanci yin takara, imma na mukamin gwamnati ko kuma rike mukamin siyasa.

  Ya kara da cewa kotun zaben ta kaddamar da cwa takarardun da mai karar, dan takarar PDP, Lawal Adamu, wanda aka fi sani da Mista LA ya gabatar bai yi daidai da tsarin doka ba.

  Hakazalika da yake martani kan hukuncin, wani lauyan Sanata Uba Sai, Barista Suleiman Shu’aibu ya bayyana hukuncin a matsayin nasara ga dimokuradiyya.

   

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here