A Biya Ma’aikata Kudinsu Kafin Karshen Disamba – FEC

0
376

Daga Usman Nasidi.

MUN samu labari cewa majalisar zartaswa ta tarayyar Najeriya FEC ta zartar da cewa tare da ba da    umarni ga Ministar kudi, Zainab Ahmed, ta tabbatar da cewa an soma biyan ma’aikata sabon karin da aka yi kafin Disamba 31.

Ministan kwadagon Najeriya, Dakta Chris Ngige, shi ne wanda ya bayyana wannan a lokacin da ya zanta da manema labarai a fadar shugaban kasa da ke Abuja a ranar Laraba, 23 ga Oktoba, 2019.

Chris Ngige ya yi wannan jawabi ne jim kadan bayan mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ya jagoranci taron FEC na Ministoci wanda aka saba zama duk ranar Laraba a fadar Aso Villa.

Dakta Ngige ya bayyana cewa majalisar tarayyar ta cimma matsayar cewa a fara biyan ma’aikata sabon albashi na akalla N30, 000 daga yanzu har zuwa ranar Talata 31 ga Watan Disamban 2019.

Bayan haka Ministan ya sanar da cewa sabon tsarin albashin zai fara aiki ne daga ranar 18 ga Watan Afrilu. Hakan na nufin ma’aikata za su bi gwamnati bashin duk wadannan tarin watanni.

Ministan harkokin jirgin sama, Hadi Sirika ya bayyana cewa an yi na’am da Naira biliyan 1.7 da aka ware domin wasu ayyuka da za a yi a filin hawa da tashin jirgin sama da ke Zariya da Katsina

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here