Adam Zango Ya Kashe Naira Miliyan 46.75 Wajen Daukar Nauyin Karatun Dalibai 101

0
696

Daga Usman Nasidi.

FITACCEN jarumin masana’antar shirya fina-finan Hausa,wato Kannywood Adam A. Zango, ya dauki nauyin karatun yara 1010 a makarantar ‘Professor Ango Abdullahi International School’ da ke garin Zariya.

Babban jami’in kamfanin shirya fina-finai na Adam Zango, wato ‘Prince Zango Production Nigeria Limited’, ya biya makarantar miliyan N46.75 a mastayin kudin daukar nauyin daliban na tsawon shekaru uku.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na dandalin sada zumunta (Instagram), Zango ya bayyana cewa, ” ina jin dadin samun damar taimakon masu karamin karfi. Yana daga cikin burin rayuwata na taimaki jama’a, musamman kananan yara, ina jin dadin yin hakan, saboda yana saka ni farin ciki.

“Ni da kamfanina kan taimaka wa jama’a ta hanyoyi da dama, ba za mu boye ayyukan alherin da muke yi ba, kuma za mu ci gaba da tallafa wa rayuwar mata, yara marasa galihu da sauran talakawa da ke fadin Najeriya.

Jarumi Adam Zango na daga cikin jaruman masana’antar Kannywood 7 da rahotanni suka bayyana cewa sun zama attajiran masu kudi.

Shugaban makarantar, Malam Hamza Jibril, ya tabbatar wa da manema labarai cewa jarumin ya biya kudin daukar nauyin daliban.

Ya ce “Eh, da gaske ne Adam Zango ya dauki nauyin karatun yara 101 a makarantarmu.Yawancin yaran marayu ne da kuma marasa karfi,” a cewarsa.”

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here