An Kai Wa Tawagar Kwankwasiya Hari A Jihar Kano Tare Da Kona Motoci 10

  0
  766
  Wani taro na 'yan Kwankwasiya

  Rabo Haladu Daga Kaduna

  RAHOTANNI daga jihar Kano, sun bayyana cewa mutane da dama suka jikkata yayin da Sanata Rabi’u Musa kwankwaso yake kaddamar da bude Kwalejin Lafiya da Unguwar Zoma ta mata zalla mai suna Nafisatu College of Nursing and Midwifery, wanda Kwankwaso ya gina a garin Madobi.

  ‘Yan Dabar wadanda ake zargin cewa daga fadar gwamnatin jihar aka turo su, sun kai harin ne ga mahalarta taron a jiya Litinin, inda nan suka fara sarar mahalarta taron da adduna da wukake, Lamarin da ya kai ga an kwashi wasu zuwa asibiti domin ba su agajin gaggawa.

  Kwalejin wacce Kwankwaso ne ya ginata a karamar hukumar Madobi da ke cikin jihar, da zimmar tallafa wa dalibai mata domin samun ilimin lafiya da ungo-zoma.

  Majiyarmu ta shaida mana cewa ‘yan dabar sun fara tare masu zuwa wurin taron tun daga unguwar Sabon Titi kan hanyar zuwa Madobi ne wanda suka rinka sararsu da adduna da wukake.

  A wata sanarwa da mai magana da yawun T

  tafiyar kwankwasiyya Sanusi Bature, ya ce mutane da dama sun jikkata wanda yanzu suna kwance a asibitoci daban-daban domin amsar magani.

  Ya ce akalla mutoci 10 ‘yan ta’addar suka lalata baya ga jikka mutane da bata dukiyarsu.

  Kwankwaso ya kaddamar da makarantar a ranar da yake murnar cika shekaru 63 da haihuwa a duniya.

  Sai dai kuma a tabakin kakakin rundunar ‘yan sandar jihar Kano Abdullahi Haruna ya ce har yanzu ba su samu wani rahoto a kan rikicin ba.

   

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here