JABIRU A HASSAN,Daga Kano.
MANOMAN shinkafa a jihar Kano sun bayyana cewa kungiyar manoma shinkafa ta kasa wato RIFAN tana kokari wajen ganin noman shinkafa a jihar ya bunkasa bisa manufofin gwamnatin tarayya na wadata kasa da abinci.
A cikin tattaunawar da wakilin mu ya yi da wasu manyan manoman shinkafa a jihar ta Kano, sun sanar da cewa ko shakka babu, kafa kungiyar ta RIFAN ya yi amfani a fadin kasar nan baki daya, kuma ana samun ci gaba mai albarka wajen rubanya noman shinkafa da sarrafa ta a jihar Kano kamar yadda ake gani.
Injiniya Sulaiman Sani, wani babban manomin shinkafa a Kano ya shaida wa Gaskiya Ta Fi Kwabo cewa kungiyar RIFAN tana kokari da gaske wajen tabbatar da ganin cewa manoman shinkafa a fadin jihar suna amfana da dukkan wani shiri na gwamnatin tarayya da ya shafi harkar noman shinkafa da sarrafa ta ba tare da samun wata matsala ba.
Sannan ya kara da cewa yanzu haka noman shinkafa ya bunkasa rani da damina a jihar kano musamman ganin yadda shugabannin kungiyar ta RIFAN suke aiki dare da rana domin ganin kwalliya tana biyan kudin sabulu ta fuskar noman shinkafa da sarrafa ta har ma da kasuwancinta a jihar cikin nasara.
Shi ma a nasa tsokacin, Alhaji Muktari Kadandani daga yankin karamar hukumar Makoda ya ce ko shakka babu, shugabannin kungiyar manoman shinkafa ta jihar Kano sun ciri tuta bisa kokarin da suke yi na ganin cewa manoman shinkafa jihar Kano suna amfana da shirin tallafa wa manoma kamar yadda ake gani tun da aka fara shirin tallafa wa manoman shinkafa tsakanin babban bankin Nijeriya wato CBN da kungiyar ta RIFAN.
Wakilinmu ya ruwaito cewa a shekara ta 2017, manoma dubu 24 ne suka amfana da shirin tallafa wa manoman shinkafa daga yankuna 8, lokacin noman rani, kana manoma dubu 44 ne suka amfana da tallafi a shekara ta 2018 da damina daga yankuna 11, yayin da manoman shinkafa dubu 28 suka sami wannan tallafi a shekara ta 2019 da rani daga yankuna 7 duk da dumbin kalubalen da ake fuskanta na aiwatar da shirin ba da tallafin daga wadanda ba su fahimci yadda tsarin yake ba