Masari Ya Bukaci Limamai Da Malamai Su Fadakar Kan Kalaman Zaman Lafiya

0
399

Mustapha Imrana Abdullahi

GWAMNA jihar Katsina Alhaji Amimu Bello Masari ya kara jaddada bukatar da ke akwai na ganin shugabannin addini da suka hada da Malamai da sauran shugabannin kan himmatuwa game da irin kalaman da ya dace a furta

Masari ya ce ba daidai ba ne a rika furta kalaman da za su iya yin jagorancin rarrabuwar kawunan jama’a musamman al’ummar musulmai.

Alhaji Aminu Bello Masari ya bayyana hakan ne a wajen taron bude “MAKON SHEHU” da ya gudana a dakin taro na hukumar kula da kananan hukumomin jihar Katsina da ke kan titin Kaita  cikin garin Katsina.

Gwamnan ya kuma bayyana fatan cewa makon na shehu ya yi jagoranci wajen hadin kan al’ummar Musulmi baki daya da za a iya samun zaman lafiya da kaunar juna a kodayaushe.

Ya bayar da shawara cewa takardu da kuma maganganun fadakarwar da za a yi a wurin za su kauce wa duk wani nau’in rabuwar kan Musulmi kasancewar hadin kai taimakon juna tare da zaman lafiyar Musulmi ne kawai aka sa a gaba.

A hannu daya kuma ya fadakar da malamai game da abin da ya dace na fadakar da Fulani da ke cikin daji da suke da karancin ilimin zamani da kuma na addinin Islama.

Kamar yadda ya bayyana cewa ya fahimci cewa a halin yanzu Fulani na kokari ne kawai na su bar wa ‘ya’yansu gadon rike bindiga a madadin yin kiwon shanu kamar yadda aka san su da yi tun asali.

Ya kuma bayar da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta taimaka wa shugabannin al’umma da na addini domin dawo da Kataina kamar yadda aka santa a can baya na wurin zaman lafiya da kaunar Juna

Gwamnan ya shawarci shugabannin gargajiya da su taimaka wajen shata kan iyakoki kamar yadda suke a da can domin rage matsalolin manoma da makiyaya.

Ya ce gwamnati za ta iyakar kokarin ta domin rage matsalar yaduwar makamai tare da miyagun kwayoyi daga shiga cikin dazuka

A nasa Jawabin mai martaba sarkin Kataina Alhaji Abdulmumini Kabir kira ya yi ga al’ummar Musulmi game da batun hadin kai da taimakon juna.

Ya ci gaba da yin godiya ga bangaren ‘yan darikar Tijjaniyya kan irin hadin kan da suke ba hukumomin gwamnati baki daya.

Shugaban kwamitin shirya taron Malam Abdul’aziz Mashi, tabbaci ya bayar na cewa dukkan bayanan da za a yi za su kasance ne kan irin fahimtar bangaren Tijjaniyya

Sai ya yi godiya ga Gwamna Masari da Sarkin Kataina kan irin yadda suke bayar da hadin kai a koda yaushe wajen ganin ci gaban bangaren na Tijjaniyya.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here