‘Yan Sanda Sun Gurfanar Da Mutumin Da Ya Kashe Mata 10

0
410

Daga Usman Nasidi.

RUNDUNAR ‘yan sandan Najeriya ta gurfanar da wani mutum mai suna Gracious David-West bayan ya amsa cewar ya kashe Mata 10 kamar yadda ake zarginsa da aikatawa.

Da yake magana a gaban alkalin kotun da aka gurfanar da shi bayan an gurfanar da shi, David-West ya ce, “mai girma mai shari’a, na kashe mata guda 9 a Otal, sai wata guda daya, cikon ta 10, wacce ban samu ikon kashe ta ba, amma na daure ta a jikin kujera.”

Sai dai, ya nemi afuwa bayan ya amsa laifuka 9 daga cikin 10 da ake tuhumarsa da aikatawa tare da bayyana cewa ya aikata laifukan ne bisa rudin shaidan.

David-West ya bukaci kotun ta umarci rundunar ‘yan sanda ta mayar masa da kudinsa N60,000, sarka da agogonsa da suka kwace a hannunsa.

Yanzu haka gwamnatin jihar Ribas, a karkashin ofishin kwamishinan shari’ar, Zacchaeus Adango, ta karbi ragamar ci gaba da shari’ar tuhumar David-West.

Alkalin kotun, Jastis Enebeli, ya amince da bukatar gwamnatin jihar tare da lasar takobin ganin ba a samu tsaiko a shari’ar ba kafin daga bisani ya daga sauraron shari’ar zuwa ranakun 18, 21, 27 da 29 ga Nuwamba, yayin da za a ci gaba da tsare David-West a gidan yari

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here