An Dakatar Da Sakatarorin Ilimi,Daraktoci Da Ma’aji A Jihar Bauci

0
463
Mustapha Imrana Abdullahi
SAKAMAKON matsalar rashin samun lambobin bankin ajiyar wadansu ma’aikatan bangaren kula da lafiyar jama’a a jihar Bauci a halin yanzu, gwamnatin jihar ta dauki matakin dakatar da wadansu manyan jami’an na baki dayan kananan hukumomi ashirin (20) da ke jihar.
Kamar dai yadda sanarwar ta bayyana daga gwamnatin jihar da kwamishinan yada labarai ya fitar cewa, an dauki matakin dakatar da sakatarorin ilimi,daraktocin bangaren kula da lafiyar jama’a tare da ma’ajin kudinsu na baki dayan kananan hukumomi ashirin (20) na jihar
Wannan dakatarwa za ta ci gaba da aikin ne har sai an tabbatar da samun sakamakon binciken da ake yi game da batun lambobin asusun ajiyar kudi a banki da ake kira (BVN) da kowa ne mai ajiya a banki yake da su domin tabbatar da sirrin ajiyarsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here