Ruwa Ya yi Awon Gaba Da Mutane 2 A Gadar Hayin Malam Bello Kaduna

0
899

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

A SAKAMAKON ruwan sama mai karfi wanda ya jima ana yi a ranar Lahadin nan, wasu mutanen dake cikin keke Napep su hudu, sun afka a cikin rafin gadar Hayin Malam Bello dake Rigasa Kaduna, inda ruwan ya yi awon gaba da wata yarinya da mai ceton ta ba a gansu ba.

Lamarin wanda ya auku da marecen ranar lahadin ayayin da ake dan yayyafi bayan ruwan ya dan tsagaita amma ruwan da aka yi yake ta kai kawo yana gudana har ta saman gadar, wanda ruwan ya yi sanadin afkawar keke Napep din wanda ke dauke da mata uku da yaro namiji daya a cikin rafin ayayin da shi mai keken ke kokarin ketarewa.

Farida Saminu kenan wacce ba a ganta ba

Rahotanni sun bayyana cewa daya daga cikin matan wacce aka bayyana sunanta da Farida Saminu da wani mai gyaran Babura Abdullahi wanda ya yi kokarin ceto ta ne kadai ba a samu yin nasarar ganin su ba, ayayin shi Albdullhi da al’umma makusanta kusa da wajen suka yi kokarin kai masu agaji ayayin da sauran matan biyu da yaron namijin da mai keken suka samu tsira bayan mutane sun kai musu agaji lokacin da ruwan ya yi gaba dasu.

Wata majiya ta bayyana wa wakilinmu cewa shi Abdullahi ya yi kokarin kaiwa ita wannan baiwar Allah agaji ne ta hangar yin nitso ya yi iyo cikin ruwan, toh amma Allah baisa ya yi nasarar ceto ta ba ayayin shi ma ruwan ya yi gaba da shi.

Ita dai wannan yarinyar, bincike ya tabbatar da cewar a ranar lahadin da lamarin ya auku da ita ana saura kwanaki biyar ne auren ta, kuma ta fita ne yawon rabon katin auren ta ga yan uwa da abokan arziki ayayin da wannan iftila’in ya auka mata a hanyarsu ta komawa gida.

Majiyar ta kara da cewa shi kuwa matukin keken da sauran mutanen sun samu nasarar ketarewa ne ta hanyar makalewa kamin jama’a mazaunin kusa da gadar tare da shi bakanikin wanda yake kanikanci a wajen ya yi nitson bin ita wannan daya yarinyar, toh amma daga karshe aka rasa ganin su gaba daya.

Ta ce ” alalhakila wannan lamarin wani babban abu ne domin jama’a na kallon yadda ruwan ke juyi dasu dukda yake mutane sun yi kokarin fadawa cikin ruwan don kai musu agaji inda suka bi bayansu don ganin an samu nasarar ceto mutanen daga cikin ruwan, toh amma ita wannan yarinyar da shi Bakaniken mai neman ceton nata babu labarin samun nasarar ganin su balle har a samu ceto su.”

A halin da ake ciki a lokacin, wasu al’ummar sun tara a gaba koda Allah Zaisa a samu nasarsar tsintar wannan mutanen biyu ya Allah ko a raye ko kuwa a mace idan an gansu.

Kawo izuwa lokacin da muka rubuta wannan labarin, babu wani sabon karin bayanin da aka samu dangane samun nasarar ceto su wadannan mutanen biyu.

Ubangiji Allah Ya bayyana su kuma Yasa suna da sauran kwana a gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here