Isah Ahmed Daga Jos
RUNDUNAR kungiyar tsaro ta Danga reshen karamar hukumar Toro da ke jihar Bauci, ta sami nasarar kama wasu matasa guda 5, da suka addabi al’ummar yankin da garkuwa da mutane. Shugaban kungiyar Alhaji Yusuf Abdullahi ne ya bayyana haka, lokacin da yake zantawa da wakilinmu a garin Magama Gumau.
Ya ce abin da yake faruwa ba ta gari sun dami al’ummar wannan yanki, don haka
a kullum ‘yan wannan kungiya suna sanya idanu a wurare daban-daban a yankin, don kula da yadda mutane suke kaiwa da komawa.
Ya ce sakamakon haka ne suka gano wadannan matasa masu garkuwa da mutane. Kuma sun kama mutane 3 a Gumau, mutane 2 kuma sun kama su ne a wajen Zaranda.
Ya ce daya daga cikinsu ya bayyana masu cewa sun yi garkuwa da mutane sau 7. Kuma ya bayyana masu cewa har kanen babansa sun yi garkuwa da shi, sun karbi kudi naira dubu 700.
Ya ce wadannan masu garkuwa da mutane da suka kama su ne Shagari Ibrahim da Alhassan Abdullahi da Ibrahim Sulaiman da Muhammadu Inuwa da kuma Isah Ibrahim.
Ya ce tuni sun mika wa rundunar ‘yan sandan jihar Bauci wadannan matasa da ake zargi da aikata garkuwa da mutane.
‘’Muna kira ga gwamnati ta sanya ido kan wadanda muke kamawa, domin yawanci idan mun kama irin wadannan masu laifi, ana sako su. Wannan shi ne babbar damuwarmu domin idan aka kama mai aikata laifi irin wannan aka sake shi, ba tare da an hukunta shi ba, idan ya fito zai ci gaba da aikata irin wannan laifi’’.
Ya yi kira ga iyayen kasa su kara sanya idanu kuma su ba su hadin kai, don kawo karshen wannan al’amari.
Wakilinmu ya yi kokarin kiran kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Bauci, DSP Kamal Datti domin jin ta bakinsa, kan wannan al’amari amma bai same shi ba.