Ban Taba Da-na-sanin Zuwa Cibiyar Horarwar Malam Niga Ba – Tsohon Dalibi

0
475

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

WANI tsohon dalibi Abdullahi Muhammed kuma mai aikin gadi a harabar cibiyar makarantar horar da kangararru ta Malam Niga dake Gundumar Rigasa Kaduna, ya yaba irin salon horarwar da cibiyar ke gudanarwa a sakamakon zaman da ya yi a gidan na wani dan lokaci.

Abdullahi, wanda ya kasance tsohon dalibi ne a cibiyar saboda aikin shaye-shaye, kana daga baya ya koma aikin sintiri na gadi a harabar, ya bayyana cewa bai taba yin danasanin zuwa cibiyar horar da kangararrun ba a sakamakon cigaban daya samu bayan zuwan shi gidan.

Da yake zantawa da wakilinmu, ya bayyana cewa a bisa yanayin daya tsinci kanshi ada wanda ya kassara rayuwar shi saboda shaye-shaye, babu abin da zai iya cewa akan cibiyar face yin hamdala domin irin wannan wajen shi ne yafi dacewa da duk wasu matasa da suka tsinci kansu a wani mummunar yanayi na shaye-shaye.

Ya ce “ ni dai dalibi ne, an kawo ni wannan makarantar ne saboda ina shaye-shaye da dauke-dauke kuma ina nan har Allah Yasa na gane hankali na da abin da nake sha wanda ya taba mun kai, to yanzu kuma da Allah Yasa shi shugaban ya ga na natsu, shi ne ya dauke ni aiki na gadin babura saboda ya amince dani.”

Abdullahi, ya kara da cewa a lokacin zaman shi a gidan yayin horon shi, ya koyi sana’o’i da dama wanda ya hada da sana’ar aikin Tela na Dinki da Buga Tukunya Na Karafu da aikin Fita baya ga aikin Gadi wanda yake yi kuma ake biyansa a duk wata dukda yake basa amsar kudin face sai idan suna da wata bukata tunda komai yi musu ake yi.

Acewarsa, duk sana’ar da mutum ya koya a lokacin zaman horon shi, wani abu ne wanda bayan an yaye mutum ko an sallame shi zai iya zuwa gida ya kama sana’ar shi domin wani babban abun dogaro ne ga rayuwar kowani dan adam dukda wasu tun daga nan cibiyar horarwar suke iya fara samun jarinsu da zasu dogaro da kansu.

A karshe, Abdullahi ya nuna alhenin bakin cikin shi dangane komawarsa gida akan rufe wajen domin gudun komawa abokanansa na da, kana da kuma barin aikinsa daya samu saboda baida sha’awar komawa gidan ko barin aikin daya samu a sakamakon canjin rayuwar daya samu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here