Fursunoni 153 Sun Tsere Daga Kurkukun Kogi Sakamakon Ambaliyan Ruwa

0
327

Daga Usman Nasidi.

WANI mamakon ruwan sama da ya sauka a ranar Litinin, 28 ga watan Oktoba a jahar Kogi ya lalata gidan yarin garin Koton-karfe wanda hakan ya yi sanadiyyar tserewar fursunoni 200 daga kurkukun.

Rahotanni sun bayyana cewa ruwan ya yi sanadiyyar faduwar gine-ginen da fursunonin suke zama a cikinsu yayin da ya shanye gidaje da dama a garin, sai dai wani rahoto ya nuna cewa a yanzu haka jami’an tsaro sun sake kama fursunoni 100, yayin da wasu kuma suka dawo da kansu.

Majiyarmu ta bayyana cewa tun da misalin karfe 2 na dare ne aka fara ruwan har zuwa safiyar Litinin, wanda hakan ya yi sanadiyyar ambaliyan ruwa daga rafin Osugu kamar yadda limamin babban Masallacin Koton-Karfe, Saidu Sulaiman ya bayyana.

Sai dai duk kokarin da majiyarmu ta yin a jin ta bakin gandurobobin da ke gidan yarin ya ci tura, sakamakon sun ki amincewa su yin magana da ‘yan jaridu game da aukuwar lamarin. Haka nan koda wakilin majiyarmu ya ziyarci ofishin shugaban kurkukun, ba ta tarar da kowa a wajen ba.

Amma rundunar ‘yan sandan jihar Kogin, ta ce tuni ta samu zarafin cafke fursunoni 31 daga cikin 153 da suka tsere daga gidan yarin garin Koton Karfe na jihar Kogi.

Da misalin karfe 5:00 na safiyar ranar Litinin ne dai fursunonin suka tsinke bayan da ruwa kamar da bakin kwarya ya rusa wani bangare na ginin gidan yarin.

To sai dai kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Williams Obe Aya, ya shaida cewa bayan tserewar fursunonin ne hukumar ta nemi daukin wasu hukumomi da ‘yan banga domin shawo kan fusrsunonin.

DSP Williams ya kara da cewa kawo yanzu jami’an nasu bisa hadin gwiwar ‘yan sintiri sun samu nasarar cafke mutum 31, kuma tuni aka mayar da su gidan yarin.

Sai dai ya ce jami’an nasu na ci gaba da farautar ragowar fursunoni 122 wadanda suka bazama daji

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here