Ilmin Mata Na Da Matukar Muhimmanci A Cikin Al’umma -Sheikh Jingir                              

0
545

 Isah  Ahmed Daga Jos

SHUGABAN majalisar malamai na Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah ta kasa Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir, ya bayyana cewa babu shakka ilmin mata yana da matukar muhimmanci, a cikin al’umma. Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya bayyana haka ne, a lokacin da yake jawabi a wajen taron yaye daliban makarantar koyon kiwon lafiya, ta Sahlan da ke garin Jos karo na uku, da aka gudanar a karshen makon da ya gabata.

Ya ce ilmin mace yana da matukar muhimmanci a cikin al’umma, domin mace ita ce uwa da take rainon ‘ya’ya a cikin al’umma.

Ya ce don haka ya kamata mu sanya ‘ya’yanmu mata su karanci kowanne irin fanni na ilmi, musamman ilmin kiwon lafiya.

‘’Na yi matukar farin cikin ganin irin yaranmu da wannan makaranta ta koyar da kiwon lafiya ta yaye. Babu shakka idan aka ci gaba da yin irin wannan aiki, kasarmu za ta yi kyau nan gaba. Don haka mu ci gaba da kafa irin wadannan makarantu, kuma mu ba su goyan baya’’.

Sheikh Jingir ya bayyana goyan bayansa ga matakin da gwamnati ta dauka na kawar da gidajen kangararrun da aka gina ba bisa ka’ida ba, a kasar nan.

Ya ce ganin irin abubuwan da wadannan gidaje  suke yi, ya dace gwamnati ta kawar da su. Domin abubuwan da masu wadannan gidaje suke yi ya saba wa musulunci da dokokin kasar nan.

Ya ce ya kamata gwamnati ta gina gidajen kangararru ta rika kula da su, ta samar masu  da abinci da kwararrun masu karantarwa.

A nasa jawabin Kwamishinan sufuri na Jihar Filato Malam Muhammad Muhammad Abubakar ya bayyana cewa babu shakka samar da irin wannan makaranta, wani babban abin alfahari ne ga al’ummarmu. Don haka ya zama wajibi a taimaka wa wannan makaranta, domin ta ci gaba da dorewa.

Ya ce ya kamata a sami irin wadannan makarantu a ko ina, domin akwai asibitoci a garuruwa da kauyuka ga su nan da dama ba su da ma’aikata.

Ya ce idan aka samar da irin wadannan makarantu a wurare, za a sami ma’aikatan kiwon lafiya, a dukkan asibitocin da muke da su a kasar nan.

Ya yi kira ga jama’a musamman masu hali su taimaka su gina irin wadannan  makarantu.

A nasa jawabin wani mai taimakon al’umma a garin Jos, Alhaji Abubakar Sadik Plaza cewa ya yi ilmin kiwon lafiya wani bangare ne da yake da matukar muhimmanci.

Ya yi kira ga iyaye su rika tura ‘ya’yansu zuwa irin wadannan makarantu na kiwon lafiya, domin a sami isassun jami’an kiwon lafiya a kasar nan.

Tun da farko a nasa jawabin shugaban makarantar kiwon lafiyar ta Sahlan, Malam Muhammad Shafi’u Yakubu ya bayyana cewa wannan yaye dalibai shi ne karo na uku, a wannan makaranta.

Ya ce daga lokacin da suka bude wannan makaranta zuwa yanzu, sun yaye dalibai maza da mata sama da 300. Kan fannonin kiwon lafiya daban-daban da suka hada da fannin ilmin jinya, da ilmin gwaje-gwaje da ilmin bayanai kan kiwon lafiya.

‘’Babban burinmu shi ne mu ci gaba da bunkasa wannan makaranta ta hanyar kawo wasu fannonin kiwon lafiya. Kuma muna da burin ganin mun kai ga kafa jami’a a wannan gari na Jos’’

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here