Jami’an  EFCC Sun Kama Jabun Magu

0
411

Daga Usman Nasidi.

OFISHIN hukumar yaki da rashawa ta  EFCC na yankin Fatakwal, ya sanar da cafke wani mutum da ake zargi da basaja da sunan shugaban hukumar, Ibrahim Magu. An kama mutumin ne yana barazana ga daraktocin hukumar habaka yankin Naija-Delta (NDDC) .

Wilson Uwujaren, mai magana da yawun hukumar, ya bayyana hakan ne a wata takarda da ta fito daga hukumar. Wanda ake zargin mai suna Robert Swem Terfa, ya bukaci cin hanci ne daga jami’an NDDC domin “Kashe zargin rashawa” da ake yi musu.

An cafke Terfa ne a Otal din Juanita da ke Fatakwal inda yake taro da daraktocin hukumar NDDC bayan da ya tallata musu “hanyar da zai bi wajen cire sunayensu daga cikin jerin wadanda ake zargi na hukumar”.

Wanda ake zargin, ya bayyanawa daraktocin cewa yana wakiltar Magu ne. Ya kara da tabbatar musu da cewa, za a cire sunayensu daga jerin sunayen da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba da don bincika a hukumar habaka yankin na Naija- Delta

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here