Mustapha Imrana Abdullahi
LABARI da dumi-duminsa da ke iske mu na cewa Gwamnan jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya sauke dukkan shugabannin kananan hukumomin jihar Katsina baki daya
Kamar yadda wata jaridar da ake wallafa wa a yanar gizo mai babban ofishinta a cikin garin Katsina ta ruwaito cewa, Gwamnan ya bukaci daukacin shugabannin kananan hukumomin da su mika ragamar mulkin kananan hukumomin 34 ga daraktocin mulkin kananan hukumominsu kafin karshen wannan watan 31 domin ci gaba da tafiyar da ragamar su kamar yadda yake a tsarin doka.