Jami’an Soji Sun Cika Hannu Da Masu Garkuwa Da Mutane 6 A Abuja

0
426

Daga Usman Nasidi.

DAKARUN Sojin Najeriya sun damke shugaban wata kungiyar ‘yan bindiga, Shehu Jatau, tare da yaransa biyar a wani Otal a kwaryar birnin tarayya Abuja.

Jatau da ‘yan kungiyarsa ne suka addabi birnin tarayya da fashi da kuma garkuwa da mutane.

A ranar Asabar, hukumar Sojin ta bayyana cewa binciken da aka fara kaddamarwa ya nuna cewa sun kasance masu tayar da zaune-tsaye a jihar Filato amma suka koma Abuja domin garkuwa da mutane da fashi.

Jami’in yada labarai na hukumar Soji, Kanal Aminu Iliyasu, a jawabin da ya saki ya tabbatar da damke su.

Iliyasu ya ce, “Wani kasurgumin shugaban ‘yan bindigar kabilar Tarok, Shehu Jatau, tare da abokan aikinsa biyar sun shiga hannu a sintirin da aka kai musu cikin dakin Otal cikin garin Abuja.”

Bincike ya nuna cewa ‘yan barandan sun kasance masu tayar da tarzoma a jihar Filato da aka yi asarar rayuka da dukiyoyin biliyoyin Naira.”

“Amma da aka samu zaman lafiya a jihar, sai suka koma garkuwa da mutane, sace-sace da kai wa mutane hari.”

A bangare guda, dakarun bataliyar soji ta 2 (2 Battalion) yayin da sintiri tsakanin kauyen Falwaya da Gayam a karamar hukumar birnin gwari na jihar Kaduna sun ceto mutane bakwai da aka sace.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here