Rufe Iyakoki Ya Taimaka Wajen Rage Shigo Da Makamai Najeriya – Shugaban DSS

0
359

 Daga Usman Nasidi.

SHUGABAN Hukumar Jami’an tsaron farin kaya na cikin gida (DSS), Magaji Bichi, ya ce rufe iyakokin da Najeriya da gwamnatin tarayya ta yi ya taimaka wajen rage fataucin makamai kuma ya taimaka wa jami’an tsaro wajen lura da shiga da ficen mutanen da ka iya zama kalubale ga zaman lafiyar kasa.

Mista Bichi ya bayyana hakan ne a taron yaye daliban ilimin leken asiri da Abuja.

Ya roki gwamnati ta sanyawa iyakokin katangar karfe har sai lokacin da abubuwa suka daidaita.

Ya ce: ” Kulle iyakokinmu ya fara haifar da da mai ido duk da soke-soken da ake yi. Rufe iyakokin kawo yanzu ya taimaka wajen hana fasa kwaurin kayyayaki da makami zuwa kasar. Hakazalika ya taimaka wajen lura da shiga da ficen mutanen da ka iya kawo matsalar tsaro kasar nan .”

Shugaban DSS ya yi kira ga daliban da ake yayewa su yi amfani da ilimin da suka samu a wuraren aikinsu domin taimaka wa gwamnati wajen dakile matsalolin tsaro.

Za ku tuna cewa a ranar 21 ga Agusta, gwamnatin tarayya ta rufe iyakokin Najeriya hudu domin kawo karshen fasa kwauri domin inganta tattalin arzikin kasa.

A cewar mai bai wa shugaban kasa shawara kan tsaro, Babagana Monguno, ba za a bude iyakokin ba har sai an cimma manufa.

Hakazalika Gwamnan babban bankin kasa, CBN, Godwin Emefiele, ya kwadaitar da gwamnati ta bar iyakokin a rufe har tsawon shekaru biyu masu zuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here