Adam Zango Ya Biya Naira Miliyan 46 Domin Karatun Marayu 101 A Zariya

0
899
Rabo Haladu Daga Kaduna
SHUABAN  makarantar Professor Ango Abdullahi da ke birnin Zariya, Dokta Shamsuddeen Aliyu Maiyasin, Garkuwar makarantar Zazzau, ya ce babu tantama kan naira miliyan 46 da fitaccen dan wasan Hausan nan, Adam Zango ya zuba a makarantar domin tallafa wa marayu 101 su yi karatu.
Dokta Shamsuddeen ya kara da cewa ba wannan ne karon farko ba da fitaccen jarumin yake bayar da irin wannan gudunmawa ba ga marasa karfi musamman kan abin da ya shafi karatunsu.
 Dokta Shamsuddeen Aliyu da Haruna Ibrahim Kakangi.
A ranar Laraba ne dai Adam Zango ya wallafa batun tare da rasitin biyan kudin a shafinsa na Instagram.
Wannan batu ne dai ya janyo mahawara a kafafen sada zumunta, inda da dama ke ganin Adam Zango ba shi da kudin da zai iya biya wa marayu 101 kudin makaranta na shekara uku.
To sai dai manema labarai sun tuntubi wasu na kusa da jarumin inda suka shaida  cewa “yana da gidauniya da ke neman tallafin mutane musamman masu hannu da marayu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here