An Damke Wata Mata A Tasha Tana Kokarin Guduwa Onitsha Da Yaran Hausawan Da Ta Sata

0
434

Daga Usman Nasidi.

HUKUMAR ‘yan sanda a jihar Legas ta tabbatar da damke wata mata da ta sace yara maza biyu a  Arewa a tashar motar zuwa Onitsha, jihar Anambara, kudancin Najeriya.

An damke ta ne a tashar Chemist Bus Stop da ke kusa da kasuwar Alaba a jihar Legas.

Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar, DSP Bala Elkana, ya ce matar da mijinya a yanzu na hannun hukumar ‘yan sanda.

Malam Abba Abdullahi wanda idon shaida ne ya yi bayan kamar yadda Daily Trust ta ruwaito cewa wani dattijo ne ya ga matar tare da yara biyu a tasha suna kokarin shiga motar bas zuwa Onitsha.

Ya ce: “Dattijon ya ji yaran suna Hausa, sai ya kira Sarkin Hausawan yankin wanda ke kusa da Unguwar Alaba Rago.”

Da Sarkin Hasusawan ya samu labarin, sai ya aika jami’an tsaro da fadawansa wajen kuma aka damke ta.
Bayan damketa, matar ta bayyana gaskiyar lamarin cewa wani mutum ne ya bata yaran a garin Jos.

A yanzu an dauke matar da mijinta ofishin ‘yan sanda na Ojo zuwa hedkwatar hukumar a Ikeja.

Ya kara da cewa mutane sun farga yanzu tun lokacin da aka samu labarin satar yara daga Arewa ana sayar da su a jihohin Inyamurai.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here