Idan Aka Zabi Lalong A Matsayin Mataimakin Shugaban Kasa Ya Yi Daidai -Dan Manjang

  0
  567
  Mista Dan Manjang

  Isah Ahmed Daga Jos 

  MISTA Dan Manjang shi ne  kwamishinan yada labarai na Jihar Filato. A wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu, ya yi bayanai kan kusancin Gwamnan jihar Simon Lalong, da shugaban kasa Muhammadu Buhari, da maganar cewa yana son ya yi takarar mataimakin shugaban kasa, a zaben shekara ta 2023 da tafiye-tafiyensa zuwa kasashen waje, da dai sauransu. Ga yadda tattaunawar ta kasance:- 

  GTK: Mene ne dalilin da ya sa Gwamna Lalong yake yin kusa da shugaban kasa Buhari?

  Dan Manjang: Idan Gwamna Lalong bai yi kusa da shugaban kasa Buhari ba, waye zai yi kusa da shi?  A Najeriya muna da shugaban kasa guda 2 ne?  Yanzu a Najeriya ba mu da wani shugaban kasa,  sai shugaba Buhari.

  Wato wautar da muke yi a da a Jihar Filato a shekarar 1979,  aka ce wai gwamnatin Jihar Filato ta wancan lokacin, gwamnatin jam’iyyar NPP ce, don haka ba ta je kusa da tsohon shugaban kasa Shagari ba.

  A lokacin mun san akwai abubuwa da dama da suka wuce wa Jihar Filato.

  Saboda haka shugaban kasa kowanne iri ne, ko daga wace kabila yake, ko daga wanne addini yake, ko daga wace jam’iyya yake,shugaban Najeriya ne. Don haka idan Gwamna ya san abin da yake yi, dole ne ya yi kusa da shugaban kasa. Domin ya samo wa al’ummarsa abubuwan da ya kamata su samu.

  Kuma wannan kusanci na Gwamna Lalong da shugaban kasa Buhari, al’ummar Jihar Filato sun ga amfaninsa. Domin akwai abubuwa da yawa da aka yi wa Jihar Filato, sakamakon wannan kusanci na Gwamna Lalong da shugaban kasa Buhari. Misali idan ka dubi sha’anin zaman lafiya a Jihar Filato, an yi barikin soja a Shendam da Gashishi. An kawo sojojin sama an ajiye a Kerang. Da Gwamna Lalong ba ya kusa da shugaban kasa, ba za a iya samun wadannan abubuwa ba.

  Idan ka dubi tsohon Gwamnan Jihar Filato, Jonah Jang da ya gabata. Saboda yana kusa da shugaban kasa  ne, ya sa aka bar shi ya kafa rundunar tsaro ta Operation  Rainbow. A lokacin akwai jihohi da dama da ba su sami wannan dama ba. Saboda haka shugaban kasa, shi ne uban kowa a Najeriya.

  GTK: Ana ta rade-radin cewa Gwamna Lalong yana son ya tsaya takarar mataimakin shugaban kasa, a zaben shekara ta 2023, mene ne gaskiyar wannan magana?

  Dan Manjang: Ko waye a Najeriya idan aka ba shi mataimakin shugaban kasa zai ki ne? Saboda haka masu irin wadannan maganganu, suna shaci-fadi ne kawai. Kuma masu irin wadannan maganganu, sun rasa inda za su dafa ne. Idan aka bai wa Gwamna Lalong  shugaban kasa ko mataimakin shugaban kasa sai ya ki ne?.

  Ai ba ana tsayawa takarar mataimakin shugaban kasa ba ne. Wannan aiki ne na jam’iyya, idan jam’iyya ta ga cewa mutum ya cancanta, sai ta ce wannan mutumin ne zai tsaya mana takarar mataimakin shugaban kasa, domin a tafi tare a tsira tare. Saboda haka idan al’ummar Najeriya suka ga cewa Gwamna Lalong,  ya dace ya zama mataimakin shugaban kasa, babu wata illa a ciki.

  Saboda haka mu abin alfari ne a ce an dauki Gwamna Lalong, a matsayin mataimakin shugaban kasa da zai yi takara a zaben shekara ta 2023. Idan Lalong ya zama mataimakin shugaban kasa ai ni ma zan je na shiga Villa.

  Kuma kamar yadda na fada, wannan magana ba wai maganar yana so ko ba ya so ba ne. Abu ne na jam’iyya da  jama’ar Najeriya, idan sun ga ya cancanta shi kenan.

  Amma yanzu babban abin da Gwamna Lalong ya sanya a gaba, shi ne sauke nauyin mulkin da al’ummar Jihar Filato suka dora masa ta hanyar zabensa. Don haka babban abin da ya sanya a gaba, shi ne raya Jihar Filato, domin idan wadanda za su gaje shi, suka zo kada su sami wata matsala kamar yadda aka samu a baya.

  GTK: Mene ne za ka ce kan koke-koken da wasu ‘yan jihar nan suke yi, kan yawan tafiye-tafiyen Gwamna Lalong?

  Dan Manjang: Idan Gwamna Lalong bai yi tafiya ba za a yi magana, idan ya yi tafiya za a yi magana, idan ya kwanta za a yi magana, idan ya kasa barci za a yi magana, duk abin da ka yi mutane sai sun yi magana.

  Saboda haka Gwamna Lalong zai ci gaba da yin tafiye-tafiye idan ta dauro. Ba za mu guji tafiye-tafiye ba, domin wadannan tafiye-tafiye na Gwamna Lalong suna kawo wa Jihar Filato alherai daban-daban. Akwai ayyuka daban-daban da muka samu a Jihar Filato, ta dalilin irin wadannan tafiye-tafiye. Misali idan ka  dauki hanyar Keffi za a yi tagwayen hanya, daga Keffi zuwa Akwanga zuwa Jos zuwa Gombe. Idan Gwamna Lalong ba ya tafiya, yaya za a sami wannan abu?.

  Kwanan nan sakamakon wadannan tafiye- tafiye gwamnati kasar Japan ta tallafa wa Jihar Filato, da kudi Dala miliyan 30.

  Mutanen Filato masu tunani sun ga amfanin tafiye-tafiyen Gwamna Lalong.

  GTK: Mene ne za ka ce koken da  jam’iyyar adawa ta PDP ta yi,  kan matakin da Gwamnan Lalong ya dauka, na rantsar da ‘yan takarar kujerar shugabancin kananan hukumomi na jam’iyyar APC, a matsayin shugabannin riko a kananan hukumomin da ba a yi zabe ba, a kwanakin baya.?

  Dan Manjang: Ai ba ‘yan takarar APC kadai aka rantsar ba, har da ‘yan PDP ne aka rantsar. Shugaban Karamar Hukumar Langtang ta arewa da aka rantsar tare da wadannan shugabannin kananan hukumomi na riko, ai dan PDP ne. A lokacin mulkin PDP jam’iyyar DPP ta ci zabe a wannan karamar hukuma, amma suka ki rantsar da shugaban amma ga shi lokacin Lalong ya rantsar da dan PDP da ya ci zaben.

  Kuma kafin Lalong ya rantsar da wadannan shugabannin kananan hukumomi na riko, ya bi matakai daban daban. Ya kai majalisar dokoki ta Jihar Filato an tantance su. Saboda haka Gwamna Lalong ba shi da wani laifi, kan wannan abu da ya yi.

  Kuma  ya zuwa yanzu wadannan shugabannin kananan hukumomi suna nan suna aikinsu, lafiya babu wata matsala.

  ‘Yan PDP masu wannan korafi idan ba su yi haka ba, za mu yi mamaki domin su ‘yan adawa ne. Kuma a cikin mambobin kananan hukumomin da aka rantsar akwai ‘yan PDP a ciki.

  GTK: Wadanne irin nasarori  ne kake ganin Gwamna Lalong ya samu, tun daga lokacin zuwansa zuwa yanzu?

  Dan Manjang: Babbar nasarar da Gwamna Lalong ya samu a Jihar Filato, shi ne zaman lafiya. Domin kowa ya sani an sami zaman lafiya da kwanciyar hankali, a Jihar Filato.

  A da kafin zuwan Gwamna Lalong idan karfe 5 na yamma ta yi, ba ka isa ka bar gidanka ba. A yanzu za ka kai 12 na dare kana yawonka, babu abin da zai dame ka. A da zuwa gona ya gagari al’umma, amma yanzu kowa yana tafiya gona abinci ya bunkasa, a jihar nan. Idan ka dawo bangaren masana’antu ga su nan, an bude masana’antar taki, an bude masana’antar yin ruwan kwalba a Barikin Ladi.

  Jami’ar Jihar Filato da ke Bokkos a da tana rufe ne. Amma yanzu an bude wannan jami’a dalibai sun ci gaba da karatu, har an yaye wasu sun tafi aikin yi wa kasa hidima.

  Sannan ga maganar biyan albashi ga ma’aikata, idan aka biya ma’aikaci albashi, zai taimaki dan uwansa kuma zai je ya biya kudin makaranta, zai shiga kasuwa ko shago ya yi sayayya. Ka ga kowa yana cin moriyar biyan albashin ma’aikata a jihar nan.

  Da Gwama Lalong ya zo ya samu an yi watanni 9 ba a biya albashi ba,  amma ya biya dukkan wannan albashi. Kuma ya ci gaba da biyan ‘yan fansho.

  Akwai shiri na Gwamna Lalong da za a kashe kudi naira biliyan 59 da za a yi hanyoyi da asibitoci da makarantu, a dukkan kananan hukumomin jihar Filato 17.

  Bayan ci gaba da ayyukan raya kasa da Gwamna Lalong yake yi, da aka faro a zamanin gwamnatin da ta gabata. Akwai wasu gwamnoni da suka zo suka sami rin wadannan ayyuka, da aka faro a jihohinsu ba su ci gaba da wadannan ayyuka ba. Amma Gwamna Lalong ya ci gaba da gudanar da irin wadannan ayyuka da aka faro.  Mene ne ake nema Gwamna Lalong ya yi?

  GTK: Wanne sako ko kira ne kake da shi zuwa ga al’ummar Jihar Filato?

  Dan Manjang:Sakona ga al’ummar Filato shi ne mu hada kai, mu kaunaci junanmu kirista da musulmi da ma wanda ba shi da addini, mu hada kai mu kaunaci junanmu.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here