Kotun Daukaka Kara Ta Kori Alasan Ado Doguwa Daga Majalisa

0
572

Mustapha Imrana Abdullahi Da Rabo Haladu

KOTUN daukaka kara da ke zamanta a Kaduna ta yanke hukuncin korar shugaban masu rinjaye a majalisar dokoki ta tarayya Honarabul Alasan Ado Doguwa daga majalisar baki daya.

Kotun ta yanke hukuncin ne sakamakon irin yadda dan takarar PDP ya daukaka kara bayan kammala hukuncin otun sauraren kararrakin zabe mai zamanta a Kano.

Ita dai wannan kotun ta bayar da umarnin a sake gudanar da zabe a cikin kwanakin da doka ta tanadar bayan an yanke hukunci.

Dalilan da kotun ta bayar shi ne a lokacin zabe akwai fom na rubuta sakamakon zabe sama da guda dari amma sai arba’in kawai aka fitar daga jami’an zabe kuma hukumar ta zabe ta kasa gamsar da kotu a kan wannan korafin da masu kara suka yi.

Sai kuma samun aringizon kuri’a a wasu mazabun inda aka samu yawan kuri’ar da aka kada ta fi yawan mutanen da aka tantance, bisa wadannan korafe-korafen ne Kotun ta yanke hukuncin ta kuma tharamta wa shugaban masu rinjaye a majalisar ci gaba da zama a majalisar har sai an sake zabe kamar yadda kotun ta umurta.

To sai dai yanzu haka kotun daukaka karar ta ce ta yi mamakin yadda kotun sauraron kararrakin zaben ta yi watsi da shaidun da dan jam’iyyar ta PDP ya gabatar mata.
Wannan dai na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan da wata kotun daukaka kara ta soke zaben dan majalisar Kiru/Bebeji, Abdulmuminu Jibril

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here