Matsalar Tsaro Ta Addabe Mu A Rigasa – Gamayyar Kungiyoyi

0
580

Mustapha Imrana Abdullahi Da Usman Nasidi, Daga Kaduna.

GAMAYYAR kungiyoyin kare mutuncin unguwar Rigasa da ke karamar hukumar Igabi cikin Jihar kaduna sun bayyana wa manema labarai rashin jin dadin su da irin yadda ake sace mutane ana garkuwa da su domin neman kudin fansa.

Kamar yadda sakataren gamayyar kungiyoyin Hassan Abubakar ya karanta wa manema labarai irin yadda matsalar tasu ta tsaro take a Rigasa da kuma zuwan su majalisar dokokin Jihar Kaduna domin kai korafin su gaban majalisar, sun dai bayyana cewa yawaitar satar mutane ya yi masu yawa a yankin, sun kuma bayyana cewa da suka je majalisar dokokin Kaduna ‘yan sanda sun wulakanta su ba gaira ba dalili.

Mun fita a jiya domin zuwa majalisar dokokin Kaduna saboda mu bayyana damuwarmu ga ‘yan majalisar Kaduna kuma mataimakin shugaban masu rinjaye na majalisar tare da rakiyar wadansu ‘yan majalisar sun karbe mu, mun kuma mika masu korafin mu a rubuce.

Amma bayan mun bar wurin sai motocin ‘yan sanda akalla Ashirin tare da ‘yan sanda akalla 100 dauke da makamai suka tare mu suna kiranmu da sunaye kala kala.

Amma kasancewar shi mataimakin shugaban majalisar ya shiga magamar, duk da haka ba a cimma nasarar komai na

“Sun ji wa wadansu rauni, an kama wasu musamman matan da ke cikin mu an kuma tsare wadansu da aka kama tare da tsare su na tsawon lokaci haka kawai ba gaira ba dalili, kawai domin mun je neman ‘yancin da tsarin mulkin kasa ya ba mu a rubuce”.

“Muna kira ga ‘yan sanda idan suna yin aikinsu ya dace su daina mancewa da tsarin doka, kamar yadda lamarin yake a cikin kundin tsarin mulkin kasa”.

Barista Sani Shehu ya bayyana wa manema labarai dalilan yin zanga-zangar kamar haka “Daliin yin Zanga zangar shi ne ana samun yawaitar satar mutane a wadansu yankunan Rigasa kuma babu wani tallafi ko hobbasa daga jami’an tsaro, wannan ya sa muka yi kokarin fadakar da jama’a ta hanyar zuwa majalisa domin nan ne muke da ‘yan majalisar da ke wakiltar jama’ar Jihar Kaduna baki daya.

“Ni a jiya ‘yan sanda akalla guda uku suka kama ni suna ja min wandona suka jefa ni cikin mota, amma ina son wani dan sanda ko waye ya gaya min shin wace doka ta ba ‘yan sanda damar zagin mutane idan za su yi aiki, a ko ina”.

Akalla a jiya a yankinmu na Rigasa mun samu ci gaba za a iya cewa kwalliya ta biya kudin sabulu domin mun ga ‘yan sanda da motocinsu na zagayawa.

Shugaban karamar hukumar Igabi Honarabul Jabir Khamis Rigasa ya sayi motocin jami’an tsaro ya ba su

Ofishin ‘yan sanda guda biyu ya yi kadan domin akalla akwai mutane  miliyan uku a Rigasa, don haka muna neman a canza mana wasu manya jami’an tsaron da ke wannan yankin.

“DPO wato Baturen ‘yan sanda na yankin Nariya tare da shi ake fita yin  sintiri amma na yankin Rigasa sai dai kawai wasu su fita ba tare da shi ba, don haka a canza mana wadansu jami’an tsaron, Muna kira ga shugaban ‘yan sanda na kasa”.

Kamar wurare irin Ladi Wuri, Ado Gwaram da hayin Barde da sauran su duk wurare ne da matsalar tsaron ta yi wa kamari a yankin Rigasa

“Babu wata dokar kasa da ta ce sai ka nemi izini ka bayyana damuwarka ta hanyar lumana, akwai batu daga babbar Kotun kasa cewa ba ka neman izini kafin ka yi zanga-zangar lumana, koda akwai dokar ‘yan sanda to ta saba wa tsarin mulkin kasa”.

Ina nan da idanu na da ‘yan sanda ke Jan hijabin mata suna son dole sai sun kama su ba tare da laifin komai ba.

Amma a jiya mutanen Rigasa sun samu yin barci ba tare da jin bindiga ta ko ina karkatar kamar da can baya ba, sai kuma an samu halartar jami’an tsaro ba kamar da can baya ba da akalla sati biyu ana samun harbe-harben bindiga barkatai.

Sun rubuta wadansu kalamai na korafi kamar haka ba mu barci mai dadi a Rigasa, duk yayin da matsalar tsaro ta yi yawa a wuri to, lallai ne mutane su tashi domin kare kansu da dai sauran kalamai masu aika sako.

Wani daga cikinsu mai suna Malam Auwal,ya bayyana wa manema labarai cewa shi da kansa an  kira shi da sunan barawo a jiya a lokacin da muka je majalisar dokokin Kaduna

Ko shi mataimakin shugaban majalisar dokokin Kaduna Yusuf Zailani ya ji dadi kwarai irin yadda muka gudanar da zanga-zangarmu a majalisar

Wata mai suna Hajiya Jamila, da ake wa lakabi hamshakiya ta shaida wa manema labarai cewa masu satar mutane ba su bar kowa ba maza, mata, yara kuma musamman idan akwai mace budurwa sai an ci mutuncinta sannan a sace ta a nemi kudi.

“Mutanen yankin Nariya, Maigiginya da sauran wurare da dama duk ba su da kwanciyar hankali a kullum saboda satar mutanen da ake yi a yankin.

” Da muka je majalisa mun gamu da matsalar ‘yan sanda sun rika yi mana bulala, ta yaya dan sanda mai kiyaye doka zai dubi mace ya rika zula mata bulala haka kawai”, inji Jamila mai lakabin hamshakiya.

Ta ci gaba da cewa muna kira ga Gwamnan Jihar  Kaduna  Malam Nasiru Ahmad El-rufai da ya kara a kan kokarin da yake yi domin jami’an tsaron da ke yankin Rigasa sun yi kadan, ga lamarin a cikin sati biyu matsalar tsaron ta yi yawa a yankin.

kamar yadda mai magana da yawun ‘yan sandan DSP Yakubu Sabo, ya shaida wa wakilinmu cewa wadanda suka je majalisar dokokin Jihar Kaduna domin yin korafi daga Rigasa duk da cewa suna da ‘yancin yin hakan amma akwai doka a jihar da ta ce sai an tantance ko yaya zanga-zangar take, idan ta lumana ce sai a a ba mutum ‘yancin yin hakan, amma ba a hana su ba.

“To su na farko ba su nemi izini ba, kuma a majalisar sai suka nemi dole sai wanda suke so za su gani domin ba shi korafinsu, wannan ne ya sa aka ga lallai sai jami’an tsaro sun bincika lamarin domin a tantance harkar baki daya”.

DSP Yakubu Sabo, ya ci gaba cewa bisa wannan dalili ne ya sa ‘yan sanda suka kama wadansu mutane biyu da ake ganin su ne suka shirya zanga-zangar domin su yi bayani.

Ba fa hana zanga-zangar lumana aka yi ba ga dan kasa amma akwai doka a Jihar Kaduna saboda haka mun ga ba su bi dokar ba ne ya sa aka kama mutane biyu domin su yi bayani.

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here