Aikin Gwamnati Da Kasafin Kudi Bai Shafi Talaka Ba – Ali Ndume

0
409

Mustapha Imrana Abdullahi

DAN majalisar dattawa daga Jihar Borno Sanata Ali Ndume, ya bayyana cewa har yanzu aikin gwamnati da kasafin kudin da ake yi a Nijeriya bai shafi talakawan kasa ba.

Ya ce batun aikin majalisa shi a nasa tunanin bai ki a mayar da shi na wuccin gadi ba, inda ba za a biya su kudin albashi da wasu kudade ba sai kudin zaman da majalisar za ta yi kawai.

“Kudin da ake ba harkar zartarwa duk ya fi na ‘yan majalisa baki daya, amma ba a san nasu ba sai na ‘yan majalisa kawai ake magana”.

Ya bayyana hakan ne a cikin wani shirin talbijin na farin wata, Ndume ya ce abin da ya sa yake fadin aikin bai shafi talakawan kasa ba shi ne kawai ana biyan albashi ne kawai.

Kuma a bangaren aiki kuma abin da zai shafi talakawan kasa su ne harkar tsaro, ilimi, lafiya, tituna da sauran ayyukan raya kasa amma har yanzu ana dai lalube ne kawai.

“Ta yaya ma’aikacin da yake darakta da aka san albashinsa za a gan shi da motar da ta fi karfin albashinsa na shekaru da yawa ba zai sayi motar ba amma ana cewa ya samu arziki, ko kuma a ga dan majalisa na da gidaje da yawa a Abuja babu wanda zai damu sai a rika cewa ya samu abin duniya,amma a wadansu kasashe idan ma’aikacin gwamnati ya shiga jirgin sama kuma aka gan shi a mazaunin ‘yan ajin farko a cikin jirgin za a tambaye shi ina ya samu kudin, hakan zai iya kai wa ga dauri a gidan yari to a Nijeriya fa’.

Ya ci gaba da cewa a Nijeriya ba a iya biyan albashin ma’aikata abin da zai ishe su ko a ma’aikatu masu zaman kansu ba a biyan albashin da zai ishi mutane, sabanin yadda albashin kasashen waje yake.

Ya shaidawa Umar Faruk a cikin shirin cewa albashinsa a matsayin dan majalisa naira miliyan daya ne idan kuma an cire haraji za su koma dubu dari takwas.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here