Akalla Mutane Miliyan 7 Ne Ke Bukatar Agajin Gaggawa A Borno, Yobe Da Adamawa

0
375
Muhammad Sani Gazas Chinade, Daga Damaturu
MAJALISAR dinkin duniya ta bayyana damuwar ta dangane da halin da al’umma sama da miliyan bakwai su ke ciki a jihohin Adamawa, Borno da Yobe, na matsin rayuwa, karancin abinci, ta daliln rikicin Boko Haram, wanda ya dace a dauki kwakkwaran matakan shawo kan lamarin.
Majalisar dinkin duniya, ta yi wannan furucin a cikin wata sanarwar bayanai wadda ta fitar, a ranar Jumu’a, ta hanyar ofishin babban sakataren kula da lamurran ayyukan jin kai da tallafin gaggawa, Mista Mark Lowcock, yadda ya kara da cewa, yau kimanin sama da shekara guda, ina mai kula tare da shiga cikin damuwa dangane da yadda wannan matsalar ke dada kamari a nan jihar Borno”.
“Bayan shekaru goma da fara wannan rikici na Boko Haram da sauran matsalolin tsaro da ke da alaka da shi, wanda ya tagayyara yankuna da dama. Wanda ziyarata zuwa Borno, cikin watan Satumba na 2017 da Octoban 2018, na samu damar zanta wa da jama’ar gari da yawa, wadanda matsalar ta shafa kai tsaye, wanda ko tantama babu, akwai kimanin mutum sama da miliyan bakwai wadanda ke neman daukin tallafin gaggawa- wurjanjan, a jihohin Borno, Adamawa da Yobe”.
“Kuma mun yaba da kokarin da mahukuntan Nijeriya tare da wasu kungiyoyi ke yi dangane da lamarin, tsakanin shekarar 2016 da 2018, wajen sake kwato wasu yankuna daga hannun mayakan, al’amarin da ya tilasta mutum sama da miliyan biyu yin hijira, inda suka koma gudajen su. Amma kuma ta dalilin sake rincabewar tsaron, ta kai sabbin hare-haren maharan Boko Haram din, ya kara sanya fargaba a zukatan jama’ar jihar Borno, wanda aka
samu sabbin ‘yan gudun hijira sama da 140,000, a wannan shekarar kawai. Hakan ya jawodubun-dubatar basu samu damar yin noma a wannan damina ba, lamarin da ya jefa mutane sama da miliyan uku a cikin matsalar karancin abinci”.
“Kuma karara zan iya bayyana cewa, matakan da sojoji tare da hai da sauran jami’an tsaro ke dauka wajen yaki da matsalar tsaro, ya zama dole kuma shi ne matakin da ya dace mahukuntan Nijeriya su dauka. Kuma dole sojoji su kula da jama’a a duk lokacin da za su aiwatar da wani matakin yaki da ‘yan ta’addan; wajen kiyaye abubuwan da duk zai jefa jama’a cikin tsananin rayuwa”.
“Sannan kuma, matakin soja shi kadai ba zai iya shawo kan wannan matsalar ba. Saboda haka, bisa wannan, akwai mashahurin muhimmanci gwamnatin Nijeriya ta bullo da wasu karin hanyoyin da za su taimaka a yaki matsalar, misali a shigar da hukumomi da cibiyoyi, irin su hukumar sake bunkasa yankin arewa maso gabas, wajen fadada bin hanyoyi
da manufofi tare da tunkara musababbi da asalin hargitsin, rage wa jama’a radadin
wahalhalun rayuwa da suka dabaibaye jama’a, bunkasa yankunan, sake farfado da lamurra
da ci gaban jama’a, wanda ko shakka ba na yi, idan an dauki wadannan matakan, zai haifar da da mai ido”.
“Na yi farin cikin yadda na sake samun damar kawo ziyara a nan jihar Borno a wannan makon, lamarin da ya ba ni dama wajen sake bin bahasin yadda abubuwa ke gudana, tare da sauran manyan jami’an gwamnatin tarayya, jami’an rundunar sojoji, da manyan jami’an gwamnatin jihar Borno, da sauran kungiyoyin agajin jinkai na kasa da kasa, na cikin kasa da kananan masu bayar da tllafin, a kokarin su wajen ganin ayyukan su sun shiga kowane lungu da sakon jama’a- a hakikanin gaskiya suna taka muhimmiyar rawa”.
“Saboda haka, majalisar dinkin duniya tare da hadin gwiwa da ofishin hukumar kula da ayyukan jinkai, suna bayar da dukan goyon bayan da duk ake bukata wajen samun nasarorin ayyukan tallafin da kungiyoyi ke yi a yankin arewa maso gabashin Nijeriya, tun farkon barkewar rikicin. Wanda a shekarar 2019 kadai, sun gudanar da aikin ceton rayukan jama’a sama da mutum miliyan uku da digo takwas (3.8 m).
Ya ce, wadannan kungiyoyin suna gudanar da ayyukan su kome runtsi da wahala. Ya kara da bayyana cewa, “akwai adadin ma’aikatan majalisar dinkin duniya 38 tare da sauran kungiyoyin jinkai da aka kashe tun daga 2011, wadanda mafi akasarin su yan Nijeriya ne. Sannan da karin wasu ma’aikatan bayar da agaji goma da rikicin Boko Haram ya rutsa da su, watani 18 da suka gabata, inda guda takwas suka yi batan-dabo”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here