An Yi Wa Ma’aikatan Shari’a Taron Bita A Katsina

0
394

Mustapha Imrana Abdullahi

A kokarin ganin an samar da harkokin tafiyar da Shari’a kamar yadda ya dace, ma’aikatar shari’ar Musulunci ta shirya taron kara wa juna sani na kotunan shari’ar Musulunci na kwana 2 ƙarkashin jagorancin Grand Kadi Al’hafiz Abubakar a babban ɗakin taro na kotun daukaka kara da ke katsina.

Alkalin alkalai na Jihar Katsina Kadi Al’Hafiz Abubakar kuma shugaban taron ya bayyana muhimmancin taron ga al’akalai da al’ummar jihar Katsina, ya kuma jaddada godiyarsa ga gwamnatin jihar da irin goyan bayan da take ba hukumar ma’aikatar  shari’a, ya kuma yi kira ga al’alkalan da su mayar da hankali wajen sauraren wannan bitar da ake yi masu.

A cikin jawabin mai girma Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari CFR wanda ya samu wakilcin babban mai shari’a na Jihar Barista  Ahmad El-Marzuk ya bayyana duk wani goyan baya da mai’akatar shari’ar musulunci take nema, gwamnatinsa za ta ba su domin samun ci gaban da kowa ke bukata a rayuwa.

Ya kuma yi jan hankali ga alkalan da su rika yin gaskiya da adalci tare da tsoron Allah a duk lokacin da suke gudanar da shari’a tsakanin al’umma.

Taron ya samu halartar kakakin majalissar dokokin jihar Katsina Honarabul Tasi’u Musa Maigari Zango shi da abokan aikinsa Honarabul Abduljalal Haruna Runka (shugaban masu tsawatarwa na majalisa) tare da sauran masu ruwa da tsaki a ma’aikatar shari’ar

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here