An Damke Tsohon Soja Mai Sayar Wa ‘Yan Siyasa Jarirai

0
448

Daga Usman Nasidi.

JAMI’AN sashen IRT na hukumar yan sanda karkashin DCP Abba Kyari sun damke wani tsohon Soja, Samuel Adagbo, da laifin sayarwa yan siyasan jihar Delta sabbin jarirai.
An damke Samuel Adagbo mai shekaru 73 a duniya tare da abokan aikinsa Faith Desmond, Sunday Chinedu, da Joy Monday.

Yayinda Joy Monday ta kasance mai sayarwa Samuel Adagbo jariran, Chinedu ne yayi silar sayar da yara uku, wanda Samuel Adagbo ya sayarwa wani dan siyasa mai sune Francis.

Jaridar City Round ta bayyana cewa Samuel Adagbo wanda mazaunin garin Biri ne yana da asibiti da dakin ajiye gawawwaki a jihar Delta.

Adagbo yace: ” Na shiga hukumar Sojin Najeriya a shekarar 1968 lokacin yakin basasa kuma na yi murabus a Mayun 1982. Ina aiki a makarantar koyar da aikin Ungozoma na hukumar.

A 1984, na yi rijistan asibitin mata mallaki na karkashin ma’aikatar lafiya. Ina da dakin ajiye gawarwaki a garin. Ban yi rijista ba amma ban san ya sabawa doka ba.”

Adagbo ya bayyana cewa ya sayarwa wani dan siyasa mai suna, Francis, sabbin jarirai biyu a farashin N450,000.

Hakazalika an damkeshi da wata bindiga kuma ya bayyana cewa ya sayi bindigar N235,000.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here