Dan Sanda Ya Kashe Mutum A Bikin Da Gwamna Ya Halarta

0
407

Daga Usman Nasidi.

ANA zargin wani jami’in dan sanda a Akwa Ibom da kashe wani mutum har lahira a wani biki da Gwamnan jihar, Udom Emmanuel ya samu halarta.

Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis a Ikot Ukab, karamar hukumar Nsit Ubium da ke jihar Akwa Ibom. Har yanzu dai ba a san dalilin kisan mutumin mai suna Godwin Thomas ba.

Mai magana da yawun ‘yan sandar jihar, Odiko MacDon ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Juma’a amma ya ce har yanzu ba a gano dan sandan da yayi aika-aikar ba.

“Binciken mu na farko ya nuna cewa, jami’in tsaron gidan gwamnati da ke wajen baya gurin a yain da lamarin ya faru,” kamar yadda SP MacDon ya sanar.

” Akwai jami’an tsaro daga jihar da kuma jihohin da ke da makwaftaka da jihar don tsaro a wajen bikin, ” in ji mai magana da yawun ‘yan sandan.

“A yayin da har yanzu ba a gano wanda yayi mummunan aikin ba, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Zaki Ahmed ya bada umarnin a tsananta bincike ta yanda za a hanzarta gano wanda yayi laifin don a gurfanar dashi, ” in ji shi.

Gidan gwamnatin jihar Akwa Ibom a ranar Juma’a ta ce, gwamnan ya matukar fusata da kisan Mista Thomas.

Wata takarda da ta fito daga kwamishinan yada labarai na jihar, Charles Udoh, ya kwatanta kisan da ” abun alhini ana tsaka da murna” .

Kwamishinan ya ce, gwamnan ya ba da umarni ga jami’an tsaro da su nemo tare da hukunta wanda ya yi kisan.

“A yayin alhinin da mika ta’aziyya ga iyalan wanda aka kashen, gwamnan ya kara jaddada cewa gwamnatinsa zata cigaba da tsare rayuka da dukiyoyin da ke jiharsa,” Udoh ya ce.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here