Sallamar Hadiman Osinbajo 35, Babban Hadimin Shugaban Kasa Ya Yi Tsokaci

0
308

Daga Usman Nasidi.

BABBAN hadimin shugaban kasa kan shirye-shiryen jin dadin al’umma, Barista Isma’eel Ahmad, ya tofa albarkacin bakinsa kan sallamar hadiman mataimakin shugaban kasa 35 da ake rade-radin cewa shugaba Buhari ya sallama.

A wata hira na musamman da manema labarai, Barista Isma’il ya bayyana cewa ai ba wani abu bane idan shugaban kasa ya yanke shawarar sallamarsu tunda shine ya nada su.

Yace: “Dama shi daukesu aiki, ai Buhari ne ke daukan aiki, kuma hadiman ai ba nasa bane,na Buhari ne.

Babu wanda yayi laifi, gani akayi ya kamata ayi hakan kuma wasu an turasu ma’aikatu daban-daban suna aiki. Wannan ba wani abu bane, rayuwa ce ta gwamnati kowa ya saba.”

Da aka tambaye shi ko mai yasa aka yi hakan lokacin da ake rade-radin takun saka tsakanin Buhari da mataimakinsa, Barista Ahmad yace:

“Ai bikin Magaji bai hana na magajiya, don mutane na zargi-zargi ana hasashe-hasashe sai a ce ba za’ayi aikin gwamnati ba.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here