Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Katsina Sun Kama Barawon Babbar Mota Bas

0
422

Mustapha Imrana Abdullahi

 

RUNDUNAR ‘yan sanda ta kasa reshen jihar Katsina ta samu nasarar kama wani kasurgumin barawon da ya sace wata babbar mota mai daukar mutane 32.

Kamar yadda rundunar ta fitar da sanarwar cewa sun samu nasarar ka wanda ya sace motar kirar Tayota mai daukar mutane 32 a cikin garin Katsina bayan sun kama wanda ake zarginsa kasancewa dan fashi da makami.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar da mai magana da yawun rundunar SP Gambo Isa ya fitar aka kuma raba wa manema labarai.

“Da misalin karfe 6:30 na ranar 10/11/2019 bayan wani yunkurin da jami’an tsaron rundunar suka yi sun samu nasarar kama wani mutum mai suna Ibrahim Usman mai shekaru 35 da ke Unguwar Kwari, Badawa cikin birnin Kano tare da babbar mota kirar Tayota Bas mai launin fari da ke dauke da lamaba No.AGL 869 R, da lambar inji JTGFK518604023588, an dai kama wanda ya sato motar ne a kan titin IBB cikin garin Katsina.

Kamar yadda rundunar ‘yan sandan suka bayyana cewa an sace motar ne a jiya a lamba G9 a ofishin kamfanin wayar ta fi da gidanka da ke kan titin Audu Baki a Kano, kuma ana ci gaba da bincike, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here